Header Ads

Safarar sassan jiki: An yanke wa Ekweremadu hukuncin daurin shekaru goma

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Nijeriya, sanata Ike Ekweremadu da wanda aka yi yunkurin cirewa sashen jikin nasa a kasar Ingila.


An yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai ta Nijeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa, Beatrice mai shekaru 56, hukuncin zaman gidan kurkuku sakamakon safarar sassan jiki.

Sanata Ike Ekweremadu dan shekaru 60, da matarsa, Beatrice mai shekaru 56, suna son sanya sashen jikin ne a jikin 'yarsu Sonai mai shekaru 25. 

Su din da kuma wani mutum mai suna Dakta Obinna Obeta, daga farko an yanke masu hukunci ne na hada kai domin samun kodar mutumin.

An dai bayyana wannan shari'a da itace irinta ta farko a tarihin dokokin bauta.

Ike Ekweremadu, wanda alkalin ya bayyana da "babba a cikin baki daya al'amarin" an ya ke masa hukuncin shekaru tara da watanni takwas a kurkuku.

Dakta Obinna an yanke masa shekaru goma bayan alkalin ya gano cewa yana da hannu wajen samun wanda zai bayar da sashen jikin nasa, wanda ya ke matashi, mara abin hannu kuma mai neman taimako.

Ita kuwa Beatrice Ekweremadu an yanke mata hukuncin shekaru hudu da wata shida a kurkuku domin kasancewar ta cikin al'amarin ba sosai ba.

Mutumin da aka yi niyyar cire sashen jikin nasa, wanda ya ke mara karfi ne shi mai sayar da abubuwa a kan titin Legas, an kawo sa kasar Ingila ne domin samar da koda ga diyar Ekweremadu.

Ya gudu ne domin tseratar da ransa inda ya shiga cikin wani ofishin 'yan sanda kimanin shekara daya kenan domin shaida masu abinda ya faru bayan asibitin Royal Free Hospital sun tsayar da al'amarin wanda ba na gwamnati ba da zai ci kudi Euro 80,000.

A yayin sauraron hukuncin wanda aka watsa a talabijin, Justice Johnson, ya bayyana arzuki da Ike Ekweremadu ke da shi.

Ya bayyana dan siyasar a matsayin wani mai babban ofishi mai dukiyoyi masu yawa, 'yan aikin gida, masu taimaka masa, masu yin girki da direba ba kamar wanda ake kokarin cire sashen jikin nasa ba wanda ba zai iya biyan Euro 25 na tikiti zuwa Abuja ba.

Ya bayyana cewa Obeta ya yiwa likitoci karya cewa wanda za a cire sashen jikin nasa yaron kawu ko gwaggon yarinyar sanatan ne da ke neman a sanya mata sashen jikin.

Su ukun sun bar wanda ake kokarin cirewa sashen jikin cikin "Babbar matsalar da za ta shafi rayuwar sa a kullum." Kamar yadda ya bayyana.

"Safarar mutane zuwa wasu kasashe domin cire sashen jikinsu wani nau'i na bauta ne." Kamar yadda alkalin ya bayyana.

A cikin jawabin da wanda aka yi yunkurin cire sashen jikin nasa dan Nijeriya mai shekaru 21 kuma dan kasuwa, wanda kuma ba a fadi sunansa ba domin doka, ya bayyana cewa "yana yin addu'a" kullum domin ya samu damar zuwa Ingila domin ya yi aiki ko karatu.

No comments

Powered by Blogger.