Header Ads

Sabbin hare-haren jiragen saman Isra'ila sun kashe mutum uku a Gaza

Sabbin hare-haren jiragen saman Isra'ila sun yi sanadiyyar shahadar akalla mutane uku tare da jikkata wasu goma. Baki daya yanzu yawan wadanda suka rasu ya kai mutum 33.

Harin Isra'ila na ranar Juma'a ya samu wani gini ne wanda mutane ke ciki a birnin Al-Nasr da ke Gaza.

Rahotanni sun bayyana cewa wani babban kwamandan al-Quds Brigades na cikin wadanda suka yi shahada sakamakon harin.

Dama a farkon ranar ta Juma'a, jiragen yakin na Isra'ila sun rushe wani gida baki dayansa wanda ke gabashin Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza. 

Wani wanda ke cikin wadanda harin na Al-Nasr ya shafa an bayyana sunansa da Iyad Al-Hassani, wanda babban kwamanda ne a wani bangare na kungiyar Islamic Jihad.

Ma'aikatar lafiya da ke Gaza ta bayyana cewa zuwa yanzu hare-haren na Isra'ila sun shahadantar da mutane 33, cikin harda yara shida da mata uku, tare da jikkata wasu 111.

Kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Islamic Jihad ta bayyana cewa za ta rika kai hare-hare a wurare da ke can cikin Isra'ila sakamakon hare-haren Isra'ila a kan gidaje da ke Gaza.

Kungiyar ta bayyana cewa hare-hare kan gine-ginen Isra'ila da biranen ta ba zai tsaya ba har sai ta daina hare-haren ta da siyasar ta na kashe shugabannin Falasdinawa.

Kasar Isra'ila na cigaba da kai hare-hare a zirin Gaza a cikin kwanaki hudu da suka gabata, inda ta kashe kwamandojin fafutikar ta Falasdinawa da dama.

A wajen mayar da martani, kungiyoyin fafutikar sun harba makaman roka ga biranen Isra'ila da gine-ginen ta.

Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa ya zuwa yanzu an harbo makaman roka kimanin 1,000 daga zirin na Gaza.

A ranar Juma'a, kungiyoyin fafutikar na Falasdinawa sun harba makaman roka a karon farko a yankin al-Quds tun bayan fara yakin Isra'ila a Gaza a ranar Talata.

Makaman rokokin sun samu garuruwan Isra'ila da ke kusa da Gaza, a yayin da a ranar Alhamis wani dan Isra'ila daya ya rasa ransa wasu da dama sun jikkata sakamakon wutar makamin roka a birnin Rehovot da ke Isra'ila.

No comments

Powered by Blogger.