Header Ads

Rukunin gine-ginen Isra'ila mafi girma da ke yamma da kogin Jordan ya kama da wuta

Rukunin gine-ginen Isra'ila mafi girma kuma wanda ya fi kara fadaduwa a yamma da gabar kogin Jordan da gabashin al-Quds da aka mamaye ya fuskanci gobara.

Kamar yadda Iran Press ta bayyana yadda ta ruwaito daga kafar watsa labaru ta Al jazeera, kafar watsa labarun Isra'ila ta ruwaito ranar Lahadi cewa wata babbar gobara ta faru a wani sansanin sojojin Isra'ila da ke kusa da garin Ma'ale Adumin a yamma da gabar kogin Jordan.

Rediyon sojojin Isra'ila ya sanar cewa masu aikin kashe gobara sun isa wurin kuma suna kashe wutar, inda suka bayyana cewa wannan gobarar ba ta haifar da rasa rai ko dukiyoyi ba.

Ma'ale Adumin na daya daga cikin manyan rukunin gine-ginen Isra'ila kuma wanda ke kara fadaduwa a yamma da gabar kogin Jordan da kuma gabashin Jerusalem.

Ba a yi bayani sosai dangane da wutar ba, amma mafiyawanci kafofin watsa labarun Isra'ila sukan dauko labarun da suka shafi hatsari da gobara a yankin da aka mamaye.

A jiya (Asabar) kafofin watsa labaru sun ruwaito gobara sama da 120 a garuruwan da ke kusa da zirin Gaza kuma karfin wutar ta kai ga ta shafi tashar kula da wutar lantarki na rukunin gine-ginen Isra'ila na Ashkelon. 

Kafofin watsa labarun Isra'ila sun ma sanar cewa jami'an kashe gobara sun kasa shawo kan wutar.

No comments

Powered by Blogger.