Header Ads

Rukunin farko na 'yan Nijeriya daga Sudan sun iso Abuja

Wasu daliban Nijeriya da ke Sudan da aka kwaso

'Yan Nijeriya 375 wadanda ke gujewa rikicin kasar Sudan sun iso Abuja, a matsayin rukunin farko kenan cikin wadanda gwamnati ke taimakamawa wajen kwashe su.

Wadanda aka kwaso din sun iso ne a cikin wani jirgi mallakin Air Peace da kuma na hukumar sojojin sama ta Nijeriya (NAF), wadanda suka kwaso su daga Aswan da ke kasar Misra zuwa Abuja, babban birnin kasar Nijeriya.

A yayin da jirgin Air Peace din ya kwaso 'yan Nijeriya 282, jirgin hukumar sojojin saman ta Nijeriya (NAF) 'yan Nijeriya 96 ya kwaso, kamar yadda Ministar ayyukan jin kai, Sadiya Farouq, ta bayyanawa manema labaru.

Ministar ta bayyana cewa gwamnatin Nijeriya na cikin farin ciki "Sakamakon dukkan su sun dawo cikin koshin lafiya, ba wanda ya rasa ransa, wanda shine muhimmin abu, kuma duk kokarin da aka yi bai zama mara amfani ba." 

Ta bayyana cewa kowannensu za a bashi wasu kaya da zai kula da kansa da kuma naira 100,000 wanda Gidauniyar Dangote ta dauki nauyi.

Za ma su samu 25,000 domin kira a wayoyinsu da kuma data 1.5 GB daga kamfanin sadarwa na MTN.

A yayin tarbar ta su a filin jirgin sama, akwai Ambasadan Sudan a Nijeriya, Mohamed Yousif, wanda ya bayyana cewa bai ji dadin abinda ke faruwa a Sudan ba, amma kuma ya yi farin ciki da dawowar 'yan Nijeriyan gida lafiya.

Ambasadan ya bayyana cewa halin da Khartoum ke ciki yanzu "abubuwa na daidaituwa kuma nan ba da jimawa ba sojoji za su yi iko da birnin baki daya." 

Ana dai sa ran 'yan Nijeriya 5,500 ne za su amfana daga kwasowar da gwamnatin ke yi. An dauke su ne a motocin bas daga Sudan zuwa Misra, inda daga nan ne za a kwaso su a jirgi zuwa Nijeriya.

No comments

Powered by Blogger.