Riyadh na neman a fara sufurin jiragen sama a tsakanin Saudiyya da biranen Iran
Saudi Arabiya na neman a fara sufurij jiragen sama a tsakanin birnin Damman da ke kasar, wanda birni ne da mafi yawan mutanensa 'yan Shi'a ne, da Mashhad da ke kasar Iran, a wani bangare na yunkurin gyara alaka a tsakanin kasashen biyu kamar yadda kamfanin sufurin jiragen sama na kasar Iran ya bayyana.
Maghsud As'adi, shugaban kungiyar kamfanonin jiragen sama a Iran, ya bayyana a ranar Litinin cewa fara sufurin jiragen sama zuwa birnin da ya fi kowanne birni girma na biyu a Iran, Mashhad, wanda ke arewa maso gabashin kasar kuma mai dauke da muhimman wurare a Shi'a, abu ne mai muhimmanci ga Saudi Arabiya.
As'adi ya bayyana cewa sufurin jiragen saman zai taimakawa al'ummar Shi'a a Saudi Arabiya da ke gabashin birnin na Damman.
Ya bayyana cewa hanyar za ta kara yawan masu zuwa yawan shakatawa 'yan Saudiyya zuwa biranen kasar Iran, musamman wuraren da suke a yadda aka halitta su da ke arewacin Iran.
Wannan jawabin dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan Ma'aikatar Sufurin kasar Iran ta bayyana cewa ta karbi neman izini na fara sufurin jiragen sama a hukumance daga hukumomin Saudi Arabiya na fara yin sufurin jiragen sama sau uku a sati.
Ma'aikatar a cikin watan da ya gabata ta bayyana cewa za a fara sufurin jiragen saman ba tare da la'akari da shirye-shiryen da ke tsakanin Tehran da Riyadh dangane da jigilar alhazan Iran zuwa hajji a Saudi Arabiya ba.
Jawabin na zuwa ne a yayin da ake tsaka da shirin daidaita dangantakar diflomasiyya a tsakanin Iran da Saudi Arabiya bayan yanke dangantakar a hukumance shekaru bakwai da suka gabata.
Shirin na cikin wata yarjejeniya ce wadda kasar Sin ta jagoranta a farkon watan Maci wadda ta tanaji cewa kasashen musulman biyu su dawo da huldar su ta diflomasiyya zuwa 9 ga watan Mayu.
Post a Comment