Header Ads

Rikici ya ƙara barkewa bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan

Ministan Harkokin Kasashen Wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan (a tsakiya) tare da wakilan sojojin Sudan da na RSF bayan sa hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 21 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Rikici ya kara barkewa a babban birnin kasar Sudan a ranar Lahadi 'yan awowi bayan janarorin da ke fada da juna sun amince da tsagaita wuta a cikin satin da ke tafe, wata tsagaita wuta ta baya-bayan nan wadda aka karya. Ana sa ran tsagaita wutar za ta fara aiki ne daga karfe 9:49 na dare (1945 GMT) a ranar Litinin, kamar yadda Amurka da Saudiyya suka bayyana a cikin wata sanarwa ta hadaka bayan tattaunawa da aka yi a birnin Saudiyya na Jeddah.

"Za ta kasance na tsawon kwanaki bakwai kuma za a iya kara tsawon ta bayan amincewar bangarorin biyu." Kamar yadda jawabin ya nuna. 

A cikin wani jawabi da kafar watsa labaru ta Saudi Press Agency ta wallafa a ranar Lahadi, Riyadh ta bayyana cewa an karya yarjeniyoyi da dama tun bayan da yakin ya barke a ranar 15 ga watan Afirilu.

"Ba kamar sauran tsagaita wuta da aka yi ba, wannan yarjejeniyar an yi ta ne a Jeddah kuma bangarorin biyu sun sa hannu kuma za ta samu goyon bayan Amurka da Saudiyya tare da bibiyar kasa-da-kasa kan tsagaita wuta." Kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen ta bayyana. 

Sai dai mazauna Khartoum - wadanda suka gudu daga yakin da ake yi a cikin birane kuma wadanda suke da karancin abinci da sauran abubuwa na musamman - na tunanin wannan karon ma ba za a samu wani canjin ba.

"Sun sha tsagaita wuta wadda ba su mutunta ba a baya." Kamar yadda Hussein Mohammed ya bayyana, wanda har yanzu ya ke a Khartoum North a wani wuri da mahaifiyarsa mara lafiya duk da cewa makwaftansu sun gudu. "Muna fatar wannan karon wadanda suka shiga tsakani za su rinka bibiyar tsagaita wutar domin tabbatar da cewa ta wanzu." Kamar yadda ya shaidawa kafar watsa labaru ta AFP. 

Zuwa yanzu dai, yakin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane kusan 1000 tare da raba wasu miliyan 1 da muhallansu yayin da kuma wasu miliyoyi suka makale ba tare da hanyar samun ruwa, wutar lantarki ko magani ba. Da yawa sun rabu da iyalansu da ke 'yan kilomitoci kadan, sakamakon harbe-harben bindigogi. Kamar yadda Sawsan Mohammed, wadda ke zaune a kudancin babban birnin kasar ta bayyana, tsagaita wutar - in har ta tabbata - "Zai kasance dama ta ta farko da zan ga mahaifina da mahaifiyata da ke Omdurman." Da ke tsallekan gadar da ke saman River Nile, kamar yadda ta shaidawa kafar watsa labaru ta AFP.

No comments

Powered by Blogger.