Header Ads

Rasha ta tarwatsa na'urar tsaron sararin samaniya mallakin Amurka na Patriot da ke Kiev

Hayaki ya tashi sama bayan wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai a babban birnin kasar Ukraine, Kiev.

Rasha ta bayyana cewa ta tarwatsa na'urar tsaron sararin samaniya mallakin kasar Amurka na Patriot a wani ruwan makamai masu linzami da ta yi tsawon dare da kuma hare-haren jirgin yaki mara matuki a babban birnin kasar Ukraine wato Kiev.

Sojojin Rasha, a ranar Talata, sun ce sun lalata na'urar tsaron sararin samaniyar ne da wani makami mai linzami mai suna Kinzhal. 

Makami mai linzamin zai iya daukar makamin nukiliya wanda zai iya yin nisan kilomita 2,000. A shekarar da ta gabata ne a karon farko Rasha ta yi amfani da makamin.

Bayan haka, ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa ta kai hare-hare da dama ta kasa, ruwa da sama a Kiev a safiyar ranar Talata.

Kiev ta tabbatar da hare-haren, "Ya fita daban a yawan sa - makamai masu linzami da yawa a lokaci daya." Shugaban sashen kula da sojojin da ke Kiev, Serhy Popko, ya bayyana a Telegram.

A yanzu haka, ita ma kasar Ukraine ta yi ikirarin cewa ta harbo makamai masu linzami na kasar Rasha 18, a ciki harda wasu kamai masu linzami na Kinzhal 6.

A farkon wannan watan, kasar ta Ukraine ta yi ikirarin cewa ta harbo makami mai linzami na Kinzhal a karon farko a saman babban birnin kasar ta hanyar na'urar tsaron sararin samaniya mallakin kasar Amurka na Patriot.

Kasar Rasha dai ta kaddamar da yaki a Ukraine ne a cikin watan Fabrairun shekarar da ta gabata. A yanzu haka ita ke da iko da akalla kashi shida na makwafciyar kasar ta ta.

Ta bayyana cewa kutsawar da ta yi ta zama dole domin fuskantar barazanar tsaro da alaka ta kusa tsakanin Kiev da kasashen yamma ke yi ma ta.

Tun bayan fara yakin, kasashen yamma sun rika kawo makamai na biliyoyin daloli ga kasar Ukraine, ciki har da na'urorin roka, jiragen yaki marasa matuka, motocin yaki, tankoki da na'urorin sadarwa duk da gargadin da Rasha ta sha yi na cewa taimakon da kasashen yamma ke yi a yakin zai kara tsawan rikicin ne kawai.

No comments

Powered by Blogger.