Header Ads

NiMet ta yi gargadin yiwuwar faruwar tsawa da ruwan sama mai karfi a jihohin arewacin Nijeriya

Bayan biyo bayan kula da yadda ake samun hadari mai hade da tsawa a arewacin Nijeriya, hukumar kula da yanayin sararin samaniya ta Nijeriya (NiMET) ta yi gargadi ga 'yan kasa cewa akwai yiwuwar samun ruwan sama mai karfi a cikin kwanaki masu zuwa a jihohin arewacin kasar nan.

Kamar yadda ya ke a cikin wani jawabi wanda janar manaja kuma mai kula da hulda da jama'a na hukumar, Muntari Yusuf Ibrahim, ya bayyana a ranar Alhamis, ya bayyana cewa a yanzu haka ana ganin ruwan sama mai hade da tsawa a wasu bangarorin arewacin kasar nan da suka hada da jihohin Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da Kano. Wannan ana sa ran zai yadu zuwa yammaci inda nan ma za a samu ruwan saman mai hade da tsawa a wasu biranen.

Jawabin ya kara da cewa ruwan sama mai hade da tsawa da ake gani a yanzu haka ana sa ran zai yadu zuwa yankin gabashi inda zai haifar da ruwan sama da ke hade da tsawa da kuma yiwuwar iska mai hade da ruwa wadda za ta zo bagatatan a biranen da ke jihar Filato, babban birnin tarayya, Nasarawa, Jigawa, Adamawa, Yobe, Borno, Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano da Katsina a cikin awowi 2 zuwa 6 nan gaba.

A wuraren da aka sa ran samun ruwan saman mai hade da tsawa, akwai yiwuwar iska mai karfi ta fara zuwa kafin ruwan saman, saboda haka abubuwa kamar bishiyoyi, falwaya da abubuwan da basu da tsaro sosai da gine-gine marasa karfi za su iya faduwa, saboda haka ana shawartar mutane da su kiyaye su kuma kasance a cikin gidajensu musamman lokacin da ake yin ruwan sama mai karfi domin gujewa fadowar tsawa.

Ya ma shawarci kamfanonin jiragen sama da su kasance suna sane da rahoton yanayi akai-akai daga hukumar ta NiMET domin tsara ayyukansu yadda ya kamata. Ya ma bayyana cewa matsakaici da kuma ruwa mai karfi yana iya haifar da ambaliyar ruwa, saboda haka ana bukatar mutane su dauki duk wani mataki da ya kamata. 

Ya bukaci duk wasu manajoji, hukumomi da mutane da ke kula kula da faruwar annoba da su kasance cikin shiri domin gujewar rasa rayuka da dukiyoyin jama'a a lokacin ruwan saman.

Ya tabbatar da cewa ofishin da ke kula da hasashen, (Central Forecast Office) CFO, da ke hukumar ta NiMET zai cigaba da kula da yadda yanayin ya ke tare da fitar da bayanai in bukatar hakan ta taso.

No comments

Powered by Blogger.