Header Ads

Nambar BVN da aka ba 'yan Nijeriya ba ta da ranar daina aika - CBN

Babban bankin Nijeriya (CBN) ya tabbatar da cewa nambar tantance ma'ajiyar banki wadda aka fi sani da Bank Verification Number (BVN) da aka ba 'yan Nijeriya ba ta da ranar daina amfani.

Bankin ya bayyana haka ne sakamakon rahotanni da ke nuna cewa nambar ta BVN wadda bankin tare da hadin gwiwar Nigerian Inter - Bank Settlement System (NIBSS) suka bayar na daina amfani bayan shekaru goma.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta PRNigeria ta ruwaito, a cikin wani jawabi wanda babban daraktan bankin na rikon karya a sashen sadarwa, Isa AbdulMumin, ya sawa hannu a ranar Laraba, ya bayyana cewa ba kamar yadda ake ikirari ba, "Muna so mu fayyace cewa nambar BVN da aka ba 'yan Nijeriya ba ta da ranar daina amfani.

"Da zarar an dauki hoton 'yan yatsun kwastoma kuma ya shiga cikin ma'ajiyar NIBSS, to nambar ta BVN tana nan har tsawon rayuwa."

Sai dai kamar yadda dokokin nambar ta BVN suka nuna wadda babban bankin ya bayar a shekarar 2021, kwastomomi za su iya canza wasu bayanan su bisa wasu sharudda wadanda suke a cikin kundin kuma bayan sun samu amincewar hukumomi na musamman.

"Saboda haka muna neman kwastomomin bankuna, musamman wadanda aka dauki hotunan 'yan yatsunsu, da su cigaba da amfani da nambobin wadanda nasu ne su kadai domin suna kasancewa ne a tsawon rayuwa." Bankin na CBN ya tabbatar.

No comments

Powered by Blogger.