Header Ads

Mutanen Sudan da suka bar muhallansu sun nunka zuwa 700,000 a cikin sati daya - Majalisar dinkin duniya


Yakin da ke cigaba da faruwa tsakanin shugabannin sojoji biyu a kasar Sudan ya yi matukar shafar rayuwar fararen hula, domin a yanzu yawan mutanen da suka bar muhallansu ya lunka zuwa 700,000 a cikin satin da ya gabata kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta bayyana.

Daruruwan mutane dai sun rasa rayukansu a yakin a yayin da ake tsoron faruwar fadan kabilanci a kudancin kasar inda tuni mutane 16 suka rasa rayukansu da kuma wata zanga-zanga da wata kungiya mai karfi sosai ke yi ta goyon bayan sojoji a gabashin kasar, wani yanki wanda yakin bai shafa ba.

Paul Dillon, kakakin hukumar majalisar dinkin duniya da ke kula da tafiye-tafiyen mutane a Geneva, ya bayyana cewa sama da mutane 700,000 a yanzu haka sun bar muhallansu sakamakon yakin wanda ya shiga sati na hudu da farawa.

Wannan na zuwa ne a yayin da kididdigar ta tsaya a 340,000 a ranar Talatar da ta gabata.

Mutanen Sudan da dama sun tsallaka kan iyaka ne domin su kubuta daga yakin da ake yi a tsakanin sojojin kasar a karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan da kuma abokin hamayyarsa, Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke shugabantar dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF).

 Fadan ya fi kamari a babban birnin kasar na Khartoum - kodayake sauran bangarori musamman yankin yammacin Darfur da ke makwaftaka da kasar Chadi - shima an yi yaki mai karfi a cikinsa.

Hukumar Majalisar dinkin duniya da ke kula da 'yan gudun hijira ta bayyana cewa bayan wadanda suka bar muhallansu amma suna cikin kasar, wasu mutane 150,000 sun gudu zuwa kasashe makwafta.

Mutanen da ba su bar yankunan da ake yakin ba suna fama da rashin ruwa, wutar lantarki, abinci da kuma kulawa da lafiya a cikin kasar wadda Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa sama da kashi uku na mutanen kasar na neman agaji tun ma kafin a fara yakin.

Yaki dai a kasar ta Sudan ya barke ne a tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF) a ranar 15 ga watan Afirilun shekarar 2023. Kididdigar baya-bayan nan ta nuna cewa sanadiyyar yakin mutane kusan 700 sun rasa rayukansu. An yi yarjejeniyar zaman lafiya daban-daban, amma ba wadda aka girmama a cikinsu.

No comments

Powered by Blogger.