Header Ads

Mutane 3 sun rasa rayukansu, wasu 2 sun jikkata sakamakon harbe-harben bindiga a Kansas City, Amurka

Kansas City da ke jihar Missouri ta Amurka

An ruwaito cewa an kashe mutane uku a daren ranar Asabar yayin wani harbe-harben bindiga a wani gidan da ake sayar da kayan shaye-shaye (bar) da ke Kansas City da ke jihar Missouri a kasar Amurka.

Daya daga cikin mutanen an bayyana cewa a wurin da al'amarin ya afku ya rasu yayin da daya mutumin kuma a asibiti ya rasu.

Kamar yadda kafar watsa labarun U.S NEWS ta bayyana, akwai wasu da suka jikkata da aka kai asibiti, ciki har da wani da ke cikin mawuyacin hali da kuma daya da ke cikin hayyacinsa, kamar yadda jami'in 'yan sanda na hukumar 'yan sandan Kansas City, Donna Drake, ya bayyana ta Imel. 

Jami'an 'yan sanda da dama ne dai suka shiga cikin wurin da al'amarin ya faru mai suna Klymax Lounge da ke Indiana Avenue da misalin karfe 1:25 na dare. 

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa wanda aka kashe yana cikin ginin da al'amarin ya faru ne yayin da daya kuma ke daga wajen ginin, kamar yadda Drake ya bayyana. 

Duka wadanda abin ya shafa manyan mutane ne kamar yadda 'yan sandan suka bayyana.

No comments

Powered by Blogger.