Header Ads

Mutane 22 sun rasu a hadarin jirgin ruwa na masu yawan bude ido a Indiya

Masu gudanar da aikin ceto a ranar Litinin, 8 ga watan Mayu, bayan jirgin na masu yawan bude ido ya nutse a yankin Malappuram, Kerala a kasar Indiya.

Akalla mutane 22 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin wani jirgin ruwan masu yawon bude ido a jihar Kerala da ke kudancin kasar Indiya, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Jirgin ya juye ne a kusa da wani gari wanda ke kusa da ruwa mai suna Tanur saboda an cika shi, kamar yadda karamin sufurtandan 'yan sandan yankin Malappuram, Abdul Nazar, ya bayyana. 

Mafi yawan wadanda abin ya shafa yara ne wadanda ke hutun makaranta, kamar yadda ministan ayyukan kiwon kifi da cigaban wuraren ajiyar jiragen ruwa ya bayyana. V. Abdurrahiman ya bayyanawa manema labaru cewa ana sa ran yawan wadanda suka rasu din ya karu sakamakon jirgin ruwan ya makale ne a cikin ruwan da ke da tabo kuma an kasa ciro shi domin ceto wadanda suka makale a cikin sa.

Mutane da dama ne dai suka shiga cikin neman wadanda suka makale cikin jirgin ruwan a daren ranar Lahadi, wanda ba duka ya nutse ba. Wasu na amfani da igiyoyi domin dawo da jirgin daidai a yayin da wasu kuma ke kallon cikin windunan sa.

"Mun samu jikkuna 22, a cikin su akwai mata 15 da maza bakwai." Kamar yadda wani jami'i daga ofishin 'yan sanda na Tanur ya bayyana, "Akwai kimanin mutane shida a asibiti. Ana cigaba da gudanar da aikin ceto."

Rahotannin yawan mutanen da ke cikin jirgin ruwan yayin hadarin na nuna mutane tsakanin 30 zuwa kusan 40.

Jaridar da ke yankin ta Onmanorama ta bayyana cewa mutane 11 daga gida daya, ciki harda yara uku, suka rasa rayukansu.

An tafi da mutane hudu asibiti cikin mawuyacin hali, kamar yadda kafar watsa labaru, PTI news agency, ta ruwaito Abdurahiman na fadi.

Wadanda suka tsira sun bayyana cewa mafi yawan fasinjojin ba su sanye da rigar kariya in an fada cikin ruwa.

An ayyana ranar Litinin, wato ranar da al'amarin ya afku, ta kasance ranar zaman makoki, kamar yadda PTI ta ruwaito daga wani jawabi na gwamnati.

Al'amarin dai ya afku ne a yankin Malappuram da kimanin karfe 7 na dare a ranar Lahadi, kuma jami'ai daga rundunar gaggawa domin tunkarar annoba ta kasa sun iso wurin da al'amarin ya afku, kamar yadda kakakin hukumar kula da annoba na jihar Kerala ya bayyana.

Firaministan kasar Indiya, Narendra Modi, a cikin wani sako da ya rubuta ya bayyana cewa "ya damu sakamakon rasa rayukan" inda kuma ya bayyana cewa za a biya diyya ga iyalan wadanda al'amarin ya shafa.

Da ma akan samu hadurran jirgin ruwa a kasar Indiya, inda mafi yawan jiragen ruwan ake cikasu sosai kuma ba su da isassun kayan kariya.

A cikin watan Satumbar shekarar 2020, mutane 12 suka rasa rayukansu a yayin da wani jirgin ruwa ya nutse a ruwan Godavari River da ke kudancin jihar Andhra Pradesh. A cikin watan Mayu na shekarar 2018 kuma, mutane 30 suka rasa rayukansu a yayin da wani jirgin ruwa ya yi hadari a yankin.

No comments

Powered by Blogger.