Mutane 14,670 suka rasa rayukansu a Amurka sakamakon harbe-harben bindiga a wannan shekarar - Rahoto
Wasu 'yan kungiyar "Teens for Gun Reform" da ke neman a yi sauye-sauye dangane da dokokin bindiga yayin da suke zanga-zanga a shekarar 2018 a Washington DC.
Mutane sama da 14,600, ciki kuwa harda daruruwan matasa da kananan yara, suka rasa rayukansu a Amurka sakamakon harbe-harben bindiga tun farkon wannan shekarar, kamar yadda kididdigar wata kungiya da ba mai neman riba ba ta nuna.
Sabon rahoto daga "Gun Violence Achieve" a ranar Lahadi ya nuna cewa mutane 14,670 suka rasa rayukansu sakamakon harbe-harben bindiga, a cikin su mutane 8,382 sun kashe kan su ne ta hanyar amfani da bindiga sai kuma wasu 6,288 da suka rasa rayukansu ta hanyar kisan kai, wasu su kashe su, yayin kariyar kai da sauran su.
Rahoton ya bayyana cewa yara 93, 'yan shekara 11 zuwa kasa sun rasa rayukansu sakamakon wannan al'amari yayin da kuma wasu matasa 522 'yan shekaru 12 zuwa 17.
Binciken ya nuna cewa akwai harbe-harben bindiga da aka yi sau 199 tun shigowar shekarar 2023, yayin da kuma yawan kisan jama'a na kan-mai-uwa-da-wabi ya kai 22, wanda hakan ke nuna hauhawar kashe-kashen in an yi la'akari da shekarun baya a daidai wannan lokacin.
Yawan kashe-kashen da aka yi yayin da akwai wani jami'i a wurin ya kai 487 kuma mutane 515 suka rasa rayukansu a harbin da aka yi ba da niyya ba.
An wallafa rahoton ne bayan mutane takwas sun rasa rayukansu yayin da kuma wasu bakwai, ciki har da yara, suka jikkata sakamakon harbin da wani dan bindiga mai zaman kadaici ya yi a wani shagon saye-saye a kusa da birnin Dallas da ke jihar Texas a Amurka.
Dan bindigan da ya yi harbe-harben na ranar Asabar, wanda hukumomi suka ce shi kadai ya yi harbe-harben, 'yan sanda sun kashe shi bayan ya fara harbe-harbe a wajen shagon sayayyar mai suna Allen Premium Outlet da ke Allen.
Kamar yadda jami'an yankin suka bayyana, wadanda abin ya shafa - wadanda shekarunsu suka kama daga 5 zuwa 61 - sun samu harbin bindiga kuma an tafi da su asibitin da ke yankin.
A cikin watan da ya gabata, shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya yi kira ga majalisar Congress da ta yi dokar da za ta kawo mafita ga matsalar bindiga a kasar tare da sake dawo da dokar da ta haramta amfani da makaman da za a iya kai hari da su wadda ta ke a tsakanin shekarar 1994 zuwa 2004.
Wannan kira na Biden ya gamu da rashin amincewa daga 'yan majalisar Amurka na karkashin jam'iyyar Republican, wadanda sune manyan magoya bayan 'yancin mallakar bindiga.
Post a Comment