Makiyaya a kasar Kenya sun kashe daya daga cikin zakunan da suka fi kowanne tsufa a duniya
Wani zaki a kasar Kenya wanda aka yi imanin ya fi kowannan tsufa a daji a duniya ya mutu bayan makiyaya sun soke shi, kamar yadda jami'an da ke kula da dabbobin daji suka bayyana a ranar Juma'a.
Loonkito, wani sanannen namijin zaki dan shekaru 19, wasu Maasai Morans (jarumai) ne suka kashe shi bayan ya shiga wani garken dabbobi da ke wajen sanannen wurin shakatawa na Amboseli National Park, kamar yadda kakakin hukumar kula da dabbobin daji ta Kenya (KWS), Paul Jinaro, ya bayyanawa AFP.
"Tsohon zaki ne da ke da wasu al'amurra...Nemo abinda zai kama da kansa kuma dabbobi na da saukin samu." Jinaro ya bayyana.
"Zakin da ba ya da wata matsala zai shiga bangaren dabbobi ne da ke cikin muhallin su."
Zakuna a Afirka sukan yi rayuwa har zuwa shekaru 18 a daji, kamar yadda kungiyar da ke tattala abubuwa ta Cats for Africa ta bayyana.
KWS a shekarar 2021 ta bayyana Loonkito a matsayin "Wani mai ban mamaki a cikin iyalan maguna" wanda ya kare iyakarsa na shekaru da dama.
Kungiyar da ke tattala abubuwa ta Lion Guardians bayan mutuwar ta Loonkito, sun bayyana shi da "Alami na dagewa da kasancewa a tare."
"A cikin juyayi mu ke sanar da ku labarin mutuwar Loonkito (2004 - 2023), zakin da ya fi kowanne zaki tsufa a yankin kuma akwai yiwuwar ma a Afirka." Kamar yadda kungiyar da ba ta neman riba ta bayyana a kafar sada zumunta ta Facebook.
Rahotannin dabbobin daji da ke fadawa wuraren da mutane ke rayuwa na karuwa a kasar Kenya inda dabbobin ke kara fuskantar matsi sakamakon birane da ke kara fadi zuwa wuraren da aka bari a zamunnan baya da kuma wuraren da ake farauta.
"Mutane na bukatar a wayar masu da kai a kan yadda za su sanar da mu domin mu dauki dabbobin mu mayar da su wuraren da suke." Jami'in KWS, Jinaro, ya bayyana.
A cikin watan Yunin shekarar 2021, wani zaki ya haifar da rudani bayan ya bar muhallinsa da ke Nairobi National Park tare da shiga wani wuri mai cinkoson mutane a awowin da mutane ke fitowa domin gudanar da ayyukansu daban-daban da safe.
Muhallin da ya ke din kilomita bakwai (mil shida) ne daga tsakiyar babban birnin kasar Kenya, gudowar dabbobi daga wuraren su da ke dauke da ciyawa da yin yawo a wuraren da ke da cikowar jama'a na sama da mutum miliyan hudu ba sabon al'amari ba ne da ba a taba ji ba.
A cikin watan Disambar 2019, wani zaki ya kashe wani mutum a kusa da muhallin da zakunan suke, a yayin da a cikin shekarar 2016 an harbe wani sakamakon farmaki da raunata wani mutum da ke zaune kusa da su.
Wata daya kafin faruwar hakan, wasu zakuna biyu sun kwashe kwana daya suna yawo a cikin Kibera, wani wurin da ke cikin birni mai cinkoson jama'a, kafin daga bisani su dawo muhallansu, wasu kwanaki bayan nan an kuma ga zakuna da dama a cikin gari.
Akwai dai kimanin zakuna 2,500 a kasar Kenya, kamar yadda kididdigar farko ta dabbobi da kasar ta yi a cikin shekarar 2021 ta nuna.
Post a Comment