Header Ads

Majalisar ƙasashen musulmai ta yi kira ga ƙasashen duniya da su kawo ƙarshen zaluncin Isra'ila ga al-Quds

Majalisar kasashen musulmai ta tabbatar da ikon Falasdinawa a kan masallacin al-Quds inda ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin da zai kawo karshen zaluncin Isra'ila a birnin mai tsarki. 

A takardar karshe da ta fitar a ranar Laraba bayan kammala taron da ta yi a birnin Saudiyya na Jeddah, majalisar mai mambobi 57, ta sake bayyana cewa Isra'ila ba ta da iko a kan al-Quds da kuma wuraren shi masu tsarki na musulunci da kiristanci.

Taron ya biyo bayan kutsawa wadda za ta iya kawo fitina ne wadda ministan Isra'ila mai tsatstsauran ra'ayi kuma ministan tsaro, Itamar Ben-Gvir, ya yi ne a harabar masallacin al-Aqsa da kuma cigaba da hare-haren sojojin mamaya kan Falasdinawa.

"Kutsawar Minsitan Isra'ila harabar masallacin al-Aqsa tare da keta alfarmar sa wani abu ne na tonon fada, kuma an yi Allah wadai da shi, yana kuma nuni ne da keta dokar kasa-da-kasa da kuma tarihi da kuma matsayin al-Aqsa a doka da kuma wuraren shi masu tsarki." Kamar yadda OIC ta bayyana.

"Al'amari ne na rikici mai hatsari da ke bukatar kasashen duniya, ciki har da Majalisar Tsaro, da su yi aiki nan take domin su tsayar da shi ta hanyar matakan da za su tursasawa Isra'ila, gwamnatin mamayar, ta daina hare-haren ta kan mutanen Falasdinu, da kuma keta dokar kasa-da-kasa da kuma dokar kasa-da-kasa ta ayyukan jin kai." 

Majalisar ta tabbatar da cewa masallacin al-Aqsa wuri ne na yin ibada ga musulmai, kuma Jordanian Islamic Waqft itace ke da alhakin kula da shi.

Waqft din itace ke kula da harabar masallacin al-Aqsa a karkashin wata yarjejeniya wadda aka yi inda aka bayyana cewa musulmai ne kawai aka yarda su yi sallah a wajen.

Masu kawo ziyara wadanda ba musulmai ba an yarda su zo amma a wasu lokuta kebantattu kuma a wasu yankuna kadai.

Bayan haka, a cikin takardar majalisar ta bayyana cewa tana, "tabbatar da hakkin kasar Falasdinawa na iko kan gabashin Jerusalem da aka mamaye (al-Quds), kuma Isra'ila, gwamnatin mamaya, bata da hakki ko iko a kan birnin al-Quds da aka mamaye da kuma wuraren shi masu tsarki na musulunci da kiristanci."

A wani yunkuri na neman fada a ranar Lahadi, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi wata ganawar mako-mako na majalisar sa a wata hanya da ke karkashin masallacin al-Aqsa.

Majalisar ta OIC ta yi Allah wadai da al'amarin, tana mai cewa, "Irin wadannan al'amura na tonon fada da ba kan ka'ida suke ba, ba su da wata madogara ba dalilili ba kuma su a kan doka." 

Ta ma bayyana muhimmancin hada karfi a tsakanin kasashen na OIC wajen samar da kariya ga masallacin al-Aqsa tare kuma da goyon bayan 'yan kasar Falasdinu da ke al-Quds yayin da suke fuskantar tsare-tsaren Isra'ila na zalunci wadanda ke da niyyar yin iko da birnin, canza alamunsa na Larabawa da kuma tarihinsa da kuma matsayinsa a doka.

Majalisar ta yi kira ga kasashen duniya da "Su tursasawa Isra'ila ...ta daina keta ka'idoji, ciki har da na fadada muhallanta da kuma duk wasu matakai da ke da niyyar canza matsayin doka da tarihin masallaci mai albarka na al-Quds, wanda wannan zai sa abubuwa su tabarbare ne a yankin." 

Ya kamata a yi kokari, kamar yadda ta bayyana, wajen samar da zaman lafiya mai dorewa da samar da mafita ta kasashe biyu da ake ikirari wanda ke tabbatar da kafa kasar Falasdinawa mai 'yancin kan ta a kan iyaka ta 1967 wadda gabashin al-Quds ne babban birnin ta.

No comments

Powered by Blogger.