Ma'aikatan kasar nan sun shiga wani hali a mulkin Buhari - Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya
A cikin wata tattaunawa da BBC saboda zagayowar ranar kwadago ta duniya, sakataren Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamared Nasir Kabir, ya bayyana cewa cigaba kadan ne kawai za a iya cewa ma'aikata sun samu a karkashin gwamnati mai ci.
A cikin tattaunawar, kungiyar ta bayyana cewa ma'aikatan Nijeriya na cikin wani hali kuma babu wani sauyi na a zo a gani da aka samu tun bayan kama mulkin Buhari.
Sakataren ya bayyana cewa, "Abin farin ciki ne sake zagayowar ranar ma'aikata ta duniya, amma maganar gaskiya al'amurran da ma'aikata (a kasar Nijeriya) suke ciki da abubuwan da suke fama da su ba abin murna ko farin ciki bane."
Kwamared Nasir ya bayyana wasu abubuwa a matsayin sune manyan kalubale da ma'aikata suke fuskanta a Nijeriya, abubuwan kuwa a cewarsa sune tashin kayan masarufi, rashin isassun kudi a hannu, biyan kudin makarantar yara, tsadar wutar lantarki, tsadar man fetur da kudin kiwon lafiya.
A cewar sakataren kungiyar ta NLC, karancin albashin ma'aikata a Nijeriya ba zai ishi magidanci ya sayi buhun shinkafa da zai ciyar da iyalansa ba.
Sakataren ya bayyana cewa wuri daya da ma'aikata suka samu cigaba a lokacin mulkin Buhari shine batun biyan albashi.
"Abu daya da muka gani wanda shine za mu iya cewa za mu yabawa wannan gwamnati shine maganar biyan albashi.
"Da gaske sun biya albashi kuma suna biya babu tsaiko, amma maganar gaskiya itace albashin bai taka kara ya karya ba tunda ba ya isan ma'aikata." Kamar yadda ya bayyana.
Kwamared Nasir ya kara da cewa kungiyar NLC ba za ta kyale ba idan ta ga gwamnati ba ta yin abinda ya kamata wajen inganta rayuwar ma'aikata, inda ya bayyana cewa kowacce gwamnati da irin tsarin da takan zo da shi kuma suna sa ran gwamnatin da za a rantsar karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu za ta dauki matakin kyautatawa ma'aikata.
Post a Comment