Header Ads

Ma'aikatan jihar Zamfara sun yi sallar kunuti kan albashinsu da ba a biya ba

Wasu ma'aikata suna sallar kunuti a Zamfara

Sakamakon albashinsu da gwamnatin jiha ba ta biya ba, wasu ma'aikatan jihar Zamfara sun gabatar da sallah ta musamman domin neman taimakon Allah. 

An bayyana cewa ma'aikatan sun taru ne a masallacin Idi da ke Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara, da misalin karfe 10:00 na safe domin neman taimakon Allah kan albashin nasu da ba a biya ba.

Ma'aikatan wadanda suka koka kan wahalhalun da suke ciki sakamakon rashin biyan su albashin su, sun bayyana cewa an sa sai sun roki sadaka.

Kamar yadda ma'aikatan suka bayyana, a yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, sun ce biya na karshe da aka yi masu shine a watan Janairu kuma suna fuskantar wahala wajen samar da abubuwan bukata ga iyalansu.

"Mafi yawanmu na nema su zama mabarata, ba su iya cin abinci sau daya a rana. Saboda haka, wannan taron yin addu'o'i an yi sa ne domin neman gwamnanmu, shugaban ma'aikata, mambobin majalisar dokoki ta jiha da kuma duk wasu da abin ya shafa Allah Ya sa su ji tausayinmu.

"Mun sha wahala a wannan yunkuri da muke yi. Wasu da dama sun rasa rayukansu, ba mu so haka ya cigaba. Mun taru baki dayan mu, ba tare da kula da banbanci ba, domin mu nemi taimakon Allah a garemu baki daya." Daya daga cikinsu ya bayyana ba tare da bari a bayyana sunansa ba. 

A dai cikin watan Afirilun shekarar 2023, kafar watsa labaru ta Sahara Reporters ta ruwaito yadda gwamnatin Gwamna Bello Matawalle a jihar ta Zamfara ta biya kudaden wasu ayyuka a kananan hukumomi 14 da ke jihar, inda wasu daga cikin ayyukan aka bar su ba a karasa ba. 

Ayyukan sun hada da ginawa da sa kayyaki a cikin masaukin gwamna a kowacce karamar hukuma inda aikin ya cinye kudade ba kanana ba amma ayyukan a zahiri ba za su iya tabbatar da hakan ba.

An biya sama da kashi 80 cikin 100 na kudin ayyukan. Amma hotuna daga wuraren da ake ginawa gwamnan masauki a kananan hukumomin na nuna cewa aikin bai zo karshe ba bare kuma a yi maganar sa kayayyakin.

No comments

Powered by Blogger.