Laifin kashe matasan Falasdinawa biyu da Isra'ila ta yi a Tulkarm ba zai tafi haka ba - Kungiyoyin fafutika na Falasdinawa
Kungiyoyin fafutikar Falasdinawa na Hamas da Islamic Jihad da ke Gaza sun sha alwashin daukar fansar kashe matasan Falasdinawa biyu da Isra'ila ta yi a wani hari da ta kai a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Tulkarm a arewacin gabar yamma da kogin Jordan.
Isra'ila ta yi harin ne da safiyar ranar Asabar inda Falasdinawa biyu wadanda aka bayyana sunayensu da Samer Salah Shafiee da kuma Hamza Jamil Kharyoush, sojojin Isra'ilan suka yi masu mummunan harbi a wani kutsaya da suka yi a sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams da ke kusa da birnin Tulkarm.
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta bayyana cewa matasan guda biyu 'yan shekaru 22 an kawo su asibiti a Tulkarm ne bayan sun rasu sakamakon harbin da aka yi masu a wuya da kirji, yayin da wani kuma na uku da aka kawo aka harbe shi a kafa amma yana cikin hayyacinsa.
"'Yar mamaya Isra'ila, da tsarin siyasar ta irin na Nazi, ta dage wajen ruruta wutar rigima a yankunan da aka mamaye ta hanyar cigaba da tursasawa ga Falasdinawa, kasar su da kuma wurare masu tsarki." Kakakin Hamas, Hazem Qassem, ya bayyana a cikin wani jawabi, "Za mu cigaba da fada domin kare alfarmar wurare masu tsarki da kuma fada domin 'yancin mutanenmu."
Inda ya tabbatar da cewa laifin Isra'ila a sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams "ba zai taba wucewa ba a mayar da martani ba." Qassem ya bayyana cewa irin wannan laifin na haramtacciyar kasar Isra'ila ba zai taba hana "karuwar juyin-juya hali" na Falasdinawa ba, amma zai kara ruruta wutar juyin-juya halin ne.
A cikin wani jawabin daban, kakakin kungiyar Islamic Jihad, Tariq Salmi, ya yi Allah wadai da harin na baya-baya da Isra'ila ta kai a Tulkarm, inda ya bayyana cewa gwamnatin mamayar ta Isra'ila ita ke da "cikakken alhakin" kashe matasan Falasdinawan biyu.
"Mutanen Falasdinawa za su cigaba da sadaukarwa mai girma domin kasar su da kuma wuraren su masu tsarki, kuma wannan sadaukarwar na kara mana karfi ne da kuma dagewa wajen tunkarar mamayar." Kamar yadda ya bayyana.
Kakakin ya ce kungiyar fafutikar za ta kasance mai girmama duk wani jinin da aka shekar a kasar Falasdinawa sakamakon tursasawar Isra'ila, kuma za a nuna hakan ne ta hanyar mayar da martani kan laifuffuka, tursasawa da kuma ta'addancin masu mamayar.
Post a Comment