Kuwait ta aika da jirgin sama dauke da kayan agaji zuwa Sudan
Kasar Kuwait ta aika da jirgin sama mallakin sojojin saman kasar na biyar dauke da tan 10 na magunguna zuwa kasar Sudan wadda ke fama da fadace-fadace a ranar Litinin, 8 ga watan Mayu.
Jirgin saman shine na bayan nan da aka bayyana, karkashin umarnin gwamnatin siyasar kasar, da niyyar taimakon mutanen kasar Sudan a yayin da suke tsaka da fuskantar mawuyacin hali sakamakon fadan da ake yi a kasar, kamar yadda mai kula da hulda da jama'a na hukumar Kuwait Red Crescent Society (KRCS), Khaled Al-Zeid, ya bayyanawa kafar watsa labaru ta KUNA.
Ya ma kara da cewa kasar Kuwait za ta cigaba da tura jiragen kayan agaji kasar Sudan ta hanyar jiragen agaji, inda ya ce a shekarun da suka gabata kasar Kuwait ta taimaka sosai wajen samar da mafita kan mawuyacin halin da Sudan ta shiga sakamakon annobar da ta faru da ita.
Jami'in na KRCS ya bayyana cewa agajin na yin nuni da dangantaka mai karfi ne da ke tsakanin Kuwait da Sudan, tare da nuni da dagewar Kuwait din wajen taimakon duk wata kasa ta duniya kawai domin rawar da take takawa a bangaren agaji.
Majalisar kasar ta Kuwait ta yanke shawarar tura kayan agaji da na magani ne zuwa kasar ta Sudan a karkashin umarnin gwamnatin siyasar kasar.
Post a Comment