Header Ads

Kungiyoyin fararen hula sun yi kira ga masu arziki a Nijeriya da su tura jiragen su ƙasar Sudan domin kwaso 'yan Nijeriya

Shugaban kungiyoyin fararen hula (CSO), Awwal Musa Rafsanjani

Kungiyoyin fararen hula (CSO) a Nijeriya sun yi kira ga masu arzuki a Nijeriya da su tura jiragen da suka mallaka kasar Sudan domin su taimaka a kwaso 'yan Nijeriya da suka makale a can, musamman dalubai, gida daga kasar wadda ke fama da yaki.

Kamar yadda rahoton LEADERSHIP weekend ya nuna, kawo yanzu, babban shugaban sashen zartarwa na Airpeace, Mista Osca Onyema, ne kawai ya sadaukar da jiragen sa domin kwaso 'yan Nijeriyan wadanda ke cikin rudani daga kasar mai fama da yaki.

Sai dai a yanzu, kungiyoyin fararen hula na rokon 'yan Nijeriya masu jiragen sama da su sadaukar a kwaso 'yan kasarsu daga kasar mai fama da yaki.

CSO's din har wa yau sun yi suka dangane da rashin hanzarin gwamnatin tarayya wajen kwashe 'yan Nijeriyan da suka makale a kasar ta Sudan.

Wannan na zuwa ne a yayin da Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen kasar Misra ta bayyana cewa 'yan kasar waje mutum 16,000 ne da ke gudun yakin kasar Sudan suka ketara cikin kasar ta Misra zuwa ranar Alhamis, inda sama da 14,000 'yan Sudan ne a cikin su da suka ketaro ta hanyar kan iyakar Qustul da Arqeen, dubunnai kuma na shirin shigowa.

Fada dai ya barke ne a ranar 15 ga watan Afirilun 2023 a tsakanin sojojin kasar wadanda ke yin biyayya ga Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF) a karkashin mataimakin shugban Sudan, Mohamed Hamdan Daglo, dukkaninsu suna fada ne domin neman samun iko da mulkin kasar ta Sudan. 

Kungiyoyin fararen hular sun nuna rashin jin dadinsu da abinda ke faruwa a Sudan din tare da roko ga masu arzuki 'yan Nijeriya da su tura jiragen su da suka mallaka domin aikin kwaso 'yan Nijeriya.

Kungiyoyin sune: Transition Monitoring Group (TMG), Transparency International (TI) da kuma Civil Society Legislative Advocacy Center (CISLAC).

A yayin da suke magana ta hanyar shugabansu, Awwal Musa Rafsanjani, kungiyoyin fararen hular sun ce komene da wani zai iya yi domin a kwaso 'yan Nijeriyar da suka makale a Sudan to ya yi. 

"Ana maraba da duk wani abu da za a iya yi domin a ceto 'yan Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ta bar abinda ya ke alhakin ta ne, to wasu su taimaka.

"Muna kira ga 'yan Nijeriya, musamman masu arzuki 'yan Nijeriya, da su taimaka wajen aikin kwasowar." Cewar Rafsanjani.

"Bai dace ba a ce gwamnati da ya kamata ta kare rayukan mutane kuma a ce tana wasa ba. Wannan rashin nuna damuwa ne ga 'yan kasa da ke biyayya ga kasa da kuma gwamnati. 

" Idan gwamnati za ta iya taimakon duka 'yan Nijeriyan da wannan rikici ya rutsa da su a Sudan, za ta taimaka. Muna rokon masu arzuki 'yan Nijeriya wadanda ke da halin tura jiragen da suka mallaka da su taimaka wajen wannan kwasowa." Kamar yadda shugaban ya bayyana. 

Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta amince da samar da dalar Amurka miliyan 1.2 domin samun motocin bas 40 domin kwashe 'yan Nijeriya da suka makale a kasar ta Sudan, kuma kamar yadda ministan Harkokin Kasashen Wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama, ya bayyana za a yi amfani da kudin ne domin samun motocin bas masu kyau wadanda za su kwaso 'yan Nijeriyan da suka makale daga Khartoum a Sudan zuwa Misra, inda daga nan kuma za a kwaso su a jirgin zuwa Nijeriya.

No comments

Powered by Blogger.