Kungiyoyin fafutikar Falasdinawa sun harba makaman roka kan Tel Aviv da sauran biranen Isra'ila
Kungiyoyin fafutikar Falasdinawa sun harba makaman roka na daukar fansa biranen Isra'ila sakamakon munanan hare-haren jiragen sama da Isra'ilan ta kai a yankin na Falasdinawa, inda makaman rokan suka kai har zuwa babban birnin Isra'ila, wato Tel Aviv.
Kungiyoyin fafutikar sun bayyana cewa su ke da alhakin kai hare-haren makaman rokan Isra'ila, inda suka bayyana a cikin wani jawabi cewa sun harba "daruruwan" makaman roka zuwa yankunan da aka mamaye, ciki har da Tel Aviv, a cikin wani aiki da suka sawa suna "daukar fansar mutanen da ke da 'yanci."
"Kungiyoyin fafutika za su kasance a dunkule a kowanne yanki na kasarmu, a matsayin wani takobi da kariya ga mutanenmu, kasar mu da wurarenmu masu tsarki." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.
"Kungiyoyin fafutikar suna shirye da daukar kowanne mataki, kuma idan 'yan mamayar suka cigaba da tursasawarsu da girman kai, to su jira bakaken raneku a nan gaba." Kamar yadda jawabin ya kara da cewa.
Kafar watsa labarun Isra'ila, Channel 13, ta bayyana cewa an harba makaman roka sama da 300 daga Gaza.
Kamar yadda kafofin watsa labarun suka bayyana, an ji karar fashewar abubuwa a wurare da dama da ke zagaye da Tel Aviv.
Asibitocin Isra'ila sun bayyana cewa akalla yahudawa 'yan kama-wuri-zauna mutum biyar ne suka jikkata sakamakon wuta daga makamin roka, kamar yadda rahotanni kafafen watsa labaru suka nuna, sun ma bayyana cewa harin ya samu wani gida a Sderot.
Yayin da ta ke bayani dangane da barnar da makaman rokar suka yi, kafar watsa labaru ta Jerusalem Post ta bayyana cewa ayyukan filin jirgin sama na kasa-da-kasa da ke Tel Aviv, Ben Gurion, ya tsaya na dan lokaci sakamakon harin makaman roka daga Gaza.
Wannan harin na daukar fansa na zuwa ne a yayin da jiragen yakin Isra'ila suka cigaba da kai hare-hare wurare daban-daban da ke cikin Gaza har zuwa rana ta biyu.
Isra'ilan ta bayyana cewa ta harbi wani wuri da ake harba makaman roka wanda Islamic Jihad da mambobin ta ne ke a amfani da wurin.
Mutane hudu da suka rasu a ranar Laraba mambobin kungiyar "Popular Front for the Palestinian Liberation" ne, kamar yadda kungiyar ta bayyana a cikin wani jawabi.
Kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta bayyana, mutane 21 suka rasa rayukansu a cikin kwanaki biyu da suka gabata sakamakon hare-haren Isra'ila yayin da wasu 64 kuma suka jikkata sakamakon kutsen da Isra'ila ta yi.
Rasa rayukan da aka yi na bayan nan ya sa yawan Falasdinawa da sojojin Isra'ila suka kashe a wannan shekarar ya kusa kaiwa 130.
Post a Comment