Header Ads

Kungiyoyin fafutika na Falasdinawa sun harba makaman roka cikin Isra'ila bayan rasuwar Khader Adnan

Wasu mizayiloli da aka harba

Kungiyoyin fafutika na Falasdinawa da ke yankin zirin Gaza sun harba sama da rokoki 20 daga yankin da ke gabar ruwa zuwa yankunan da aka mamaye bayan babban shugaba a kungiyar fafutika ta Islamic Jihad, Khader Adnan, ya rasu a wani kurkuku da ke Isra'ila bayan ya kwashe kwanaki 87 yana yajin cin abinci. 

Kafofin watsa labaru na Falasdinawa a ranar Talata sun ruwaito cewa makaman roka 22 na daukar fansa aka harba a yankunan da ke dauke da jama'a da ke yankunan da aka mamaye sakamakon kisan Adnan, inda mutane uku suka jikkata daya daga cikinsu a mawuyacin hali.

An jiwo jiniyar gargadi a yankunan Sderot, Sha'ar Hanegev, Ibim da Nir Am kamar yadda kafofin watsa labaru da yaren Hebrew suka ruwaito, inda suka kara da cewa na'urar kare makamai masu linzamin Isra'ila na Iron Dome sun kabe rokoki hudu.

"Wannan shine martani na farko-farko dangane da wannan mummunan laifi da zai sa mutanenmu su yi wani abu sakamakon al'amarin." Kamar yadda kungiyoyin fafutikar da ke Gaza suka bayyana.

Wannan al'amari na zuwa ne a yayin da Falasdinawa suka shiga yajin aiki na gabadaya a gabar yamma da kogin Jordan da kuma zirin Gaza, suna kira da a fito a tunkari sojojin Isra'ila bayan kisan na Adnan.

An dai kama Khader Adnan ne a ranar 5 ga watan Fabrairu, kuma nan-da-nan ya shiga yajin cin abinci domin nuna adawa da kamun da aka yi masa.

Ya kasance yana fama da rashin lafiya mai tsanani sakamakon yajin cin abincin wanda ya hada da aman jini, rashin karfi a jiki, rashin sanin halin da ya ke ciki akai-akai, shan wahala wajen yin magana, tafiya, barci da mayar da hankali da ciwo a duka jikinsa. 

A cikin shekaru 20, sojojin Isra'ila sun kama Adnan kusan sau sha biyu sakamakon al'amurransa na siyasa da rashin goyon bayan mamaya. Ya dai yi shekaru takwas a kurkuku. 

Kungiyoyin fafutika da hukumomin Falasdinawa sun yi makokin kisan Adnan, inda suka dora alhakin wannan laifi a kan gwamnatin mamaya ta Tel Aviv.

No comments

Powered by Blogger.