Ku saurari muryoyin masu zanga-zanga, ku gujewa amfani da karfi - Iran zuwa ga gwamnatin Faransa
Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen kasar Iran ta yi kira ga 'yan sandan kasar Faransa da su gujewa amfani da karfi kan masu zanga-zanga a yayin zagaye da aka yi na ranar ma'aikata ta duniya, inda ta yi kira ga gwamnatin shugaban kasar ta Faransa, Emmanuel Macron, da ta saurari muryoyin masu adawar.
Nasser Kan'ani ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter cikin harshen Farisa a ranar Talata bayan 'yan sandan Faransa sun harba barkonun tsohuwa (tear gas) domin tarwatsa masu zanga-zanga a babban birnin kasar na Paris a ranar 1 ga watan Mayu yayin da mutanen kasar ke cigaba da nuna rashin amincewarsu dangane da canje-canje ga bangaren fanshon na Macron.
"Yin amfani da karfi da 'yan sandan Faransa ke yi a kan 'yan kasa masu zanga-zanga da ma'aikata a ranar ma'aikata ta duniya wani abu ne da baki daya ba a so faruwarsa ba." Kamar yadda Kan'ani ya rubuta, "Har yanzu muna ba gwamnatin Faransa shawarar cewa ta saurari muryoyin 'yan kasar ta masu zanga-zanga ta gujewa amfani da karfi a kan su."
Kafofin watsa labaru sun bayyana cewa 'yan sanda sun kama mutane 291 a fadin kasar yayin zanga-zangar "French Labor Day" a ranar Litinin, 111 a cikin su a birnin Paris.
Kamar yadda Ma'aikatar Cikin Gida ta kasar Faransa ta bayyana, mutane 782,000 suka gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin a fadin kasar ta Faransa domin "May Day" a wani yunkuri na nuna fusatarsu sakamakon shirin fanshon na Macron, 112,000 daga birnin Paris.
Saidai the CGT union ta bayyana cewa ta lissafa mutane miliyan 2.3 a fadin Faransa hade da wasu 550,000 a babban birnin kasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Faransa, Geral Darmanin, ya bayyanawa manema labaru cewa kimanin 'yan sanda 108 ne suka jikkata a fadin Faransa a yayin da rikici ya barke sakamakon shirin fanshon na Macron wanda ya kara shekarun Fansho daga 62 zuwa 64.
Bayan shekarun yin ritaya, dokar na neman mutane sai sun yi aiki har tsawon shekaru 43 kafin su karbi cikakken fansho, duk a cikin canje-canjen.
Bayan kotun koli a kasar Faransa ta amince da dokar, Macron ya tabbatar da ita ta hanyar sa hannu inda ya yi watsi da kiraye-kirayen jinkirta hakan, wannan kuwa shi ne ya sa mutanen kasar suka fusata tare da gabatar da zanga-zanga mafi girma a kasar cikin shekaru.
Post a Comment