Header Ads

Kotun Sweden ta ba da umarnin a kamo mutumin da ya kona Al-Kur'ani

Rasmus Paludan yayin da ya ke kona Al-Kur'ani a ranar 21 ga watan Janairun 2023 a kofar ofishin jakadancin kasar Turkiyya da ke Stockholm a kasar Sweden.

Kotun kasar Sweden ta bayar da umarnin a kamo Rasmus Paludan, wani wanda ya yi kaurin suna a kasashen Denmark da Sweden da ya keta alfarmar musulunci a watannin da suka gabata.

Rasmus Paludan, wanda shine ya kirkiro jam'iyyar kiyayya da musulunci ta Stram Kurs a kasashen Denmark da Sweden, ya kona kwafin littafi mai tsarki na addinin Musulunci, Al-Kur'ani, a yayin zanga-zanga da dama, ciki harda wadda aka gabatar a gaban ofishin jakadancin kasar Turkiyya da ke Stockholm a kasar Sweden a farkon shekarar nan.

Rahotanni a ranar Juma'a sun bayyana cewa Paludan, wanda ke aiki a matsayin lauya kuma a yanzu haka yana kasar Denmark, 'yan sandan kan iyaka za su kama shi in ya shiga kasar Sweden.

Ofishin yanke hukunci kan laifuffuka na Malmo ne suka ba da umarnin kama Paludan, wanda ya yi kaurin suna wajen kona littafin Al-Kur'ani da kuma halayya mara kyau ga kananan yara bayan wasu abubuwan, kan zarginsa da "aikata laifuffuka masu yawa" kamar yadda jaridar kasar Sweden ta Aftonbladet ta ruwaito.

Paludan, wanda ke neman a kori duk wadanda ke shigowa cikin kasa wadanda ba daga kasashen yammacin duniya suke ba tare kuma da neman hana addinin musulunci, a baya ya yi kira da a yiwa musulmai kisan kiyashi.

"Abu mafi muhimmanci da zai faru shine ya kasance babu sauran musulmi a doron duniya." Kamar yadda kafar watsa labarun Denmark ta ruwaito Paludan na fadi a yayin wata ziyara da ya kai kasar Amurka.

A kwanakin baya an bincike shi kan "harzukawa kan wasu mutane, cin mutunci da kuma hari kan wani babban jami'i" kamar yadda jaridar Aftonbladet ta kara da bayyanawa.

A kwanakin baya, Paludan ya kona kwafin littafin Al-Kur'ani a kofar ofishin jakadancin kasar Turkiyya da ke Stockholm a ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2023 a karkashin kulawar 'yan sanda daga hukumomin Sweden.

A satin da ya biyo bayan wannan, ya sake kona littafin Al-Kur'ani a kofar wani masallaci a kasar Denmark tare da bayyana cewa zai cigaba da maimaita haka a duk ranar Juma'a har sai an sa kasar Sweden cikin hadakar tsaron NATO.

Kafofin watsa labaru sun ruwaito mai yanke hukunci a kan al'amarin, Adrien Combier-Hogg, na fadin cewa rashin gaggawa a kan caje-cajen da aka shigar a kan Paludan saboda dalilin wasu matsaloli ne.

Paludan ya ki amincewa da caje-cajen da ake yi masa, ya kuma bayyana cewa ba zai je kasar Sweden ba saboda tsaro duk da cewa 'yan sandan kasar sun tabbatar da tsaron lafiyarsa.

No comments

Powered by Blogger.