Kasar Ukraine na yunkurin kashe shugaba Putin - Rasha
Sashen watsa labaru na shugaban kasar Rasha ya bayyana a ranar Laraba cewa kasar Ukraine ta yi yunkurin kashe shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a cikin daren ranar Talata ta hanyar yin amfani da jirage guda biyu masara matuka wadanda suka kai hari a muhallinsa na Kremlin.
Fadar ta Kremlin ta bayyana cewa sojoji da masu aiki na musamman sun yi amfani da na'urar yaki ta "Radar" domin hana jiragen aiki.
Kamar yadda Kremlin din ta bayyana, duk da harin da aka yi yunkurin yi, ba a samu raunuka ko asarar dukiya ba.
"Mun dauki wannan al'amari a matsayin aikin ta'addanci da aka shirya da kuma wani yunkuri a kan rayuwar shugaban kasar Rasha wanda aka yi ana gobe za a yi " May 9 Victory Parade" wanda baki daga kasashen waje suka shirya za su halarta." Kamar yadda fadar ta bayyana.
Putin ba ya cikin ginin na Kremlin lokacin harin domin yana aiki a gidan shugaban kasa na Novo-Ogaryovo da ke wajen Moscow a ranar Laraba, kamar yadda kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya bayyana.
Mai ba shugaban kasar Ukraine shawara, Mykhailo Podolyak, ya bayyanawa kafar watsa labarun gwamnati ta Ukrinform news agency cewa ba hannun Ukraine a cikin harin da aka yi ikirarin kaiwa a Kremlin.
"Ukraine ba ta kai hari Kremlin ko kuma wani wuri na Jamhuriyar Rasha ba." Kamar yadda Podolyak ya bayyana, inda ya nuna cewa sojojin Ukraine suna kai hari ne kawai a wuraren sojojin da ke wuraren da aka mamaye na dan wani lokaci mallakin Ukraine.
Ya bayyana cewa hari a wuraren Rasha, wanda ya hada da Kremlin, ba ya da wata fa'ida ga sojoji ko kuma taimakon Ukraine wajen kai hari.
Kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito, Magajin garin Moscow, Sergei Sobyanin, a ranar Laraba ya bayyana cewa an hana tashin jirage marasa matuka a babban birnin na Rasha. Kremlin ta bayyana cewa Rasha na da 'yancin mayar da martani yadda ya kamata.
Post a Comment