Header Ads

Kasar Kuwait ta aika da jirgi na 10 dauke da kayan agaji zuwa Sudan

Kasar Kuwait ta aika da jirgi na 10 wanda ke cike da kayan agaji zuwa kasar Sudan da ke fama da yaki.

Jirgin ya tashi ne daga Abdullah Al-Mubarak Air Base a ranar Asabar zuwa kasar ta Afirka kuma yana dauke ne da tan goma na kayan agaji, magunguna da tantuna, kamar yadda Khaled Al-Zaid, daraktan hulda da jama'a da bayanai na hukumar Kuwait Red Crescent Society ya bayyanawa kafar watsa labaru ta KUNA.

Daraktan ya tabbatar da niyyar cigaba da tura wasu kayayyakin agajin zuwa ga mutanen Sudan wadanda a yanzu haka ke da karancin kayan da suke wajibi ga rayuwa tare da yanayi na wahala sakamakon fadan da ake yi.

No comments

Powered by Blogger.