Header Ads

Kamfanin MTN ya canza lambobin sanya kati da na sayen data


Kamfanin Mobile Telecommunication Network, MTN, ya canza lambobin sanya kati a waya daga *555* zuwa *311*.

Kamfanin sadarwa har wa yau ya canza lambobin sayen data daga *131# zuwa *312#.

Wannan na cikin wani sako ne wanda kamfanin na MTN ya turawa kwastomominsa, sakon shine kamar haka, "Kwastoma, muna sanar da kai canza lambobin sanya kati. 

"A yanzu za ka iya sanya kati a layin ka ta hanyar amfani da *311*lambobin kati# a maimakon *555*lambobin kati#

"Muna neman da ka fara amfani da lambobin domin jin dadin ka. Mun gode domin zabar MTN."

"Kwastoma, a yanzu za ka iya sayen data ta hanyar amfani da *312# a maimakon *131#. Muna neman ka fara amfani da lambobin domin jin dadin ka. Mun gode domin zabar MTN."

Sai dai ba a bayyana dalilin canje-canjen ba.

Kamfanin sadarwar na MTN wanda ke aiki a kasashe da dama na nahiyar Afirka da Asiya, cibiyar sa na Johannesburg ne da ke kasar Afirka ta Kudu.

A cikin watan Disambar 2020, akwai masu amfani da layin na MTN mutum miliyan 280, wannan shi ya sa ya zama layin waya da ke da yawan mutane na 8 a duniya, kuma na daya a nahiyar Afirka.

Kamfanin da ke aiki a sama da kasashe 20, kudaden da kamfanin ke samu daya cikin uku daga kasar Nijeriya suke zuwa inda ya ke da kusan kashi 35 cikin 100 na kasuwa.

No comments

Powered by Blogger.