Jarabawar UTME: Wani mai zana jarabawa ya samu kashi 99% a lissafi
Master Lotanna Azuokeke, dalubi a makarantar Bishop Otubelu Juniorate, Trans Ekulu da ke Enugu ya samu maki 99 a lissafi a jarabawar shiga jami'a ta Unified Tertiary Matriculation Exam (UTME) da aka kammala.
Azuokeke, mai shekaru 15, ya samu maki 337 ne baki daya a jarabawar, kamar yadda Dr. Chiwuike Uba, mai bada shawara a bangaren sadarwa ga Bishop of the Docese of Nike (Anglican Communion), wanda ya kirkiro makarantar.
Uba ya bayyana cewa Azuokeke, wanda ke zaune a Oba da ke karamar hukumar Idemmili ta Kudu a jihar Anambra, ya samu 88 ne a "Chemistry," 86 a "Physics," sai kuma 64 a "English Language."
"Azuokeke ya kafa wani tarihin bayan tarihin da Chidera Obi ya bari na samun maki 329, inda ya zama wanda ya fi kowa maki, shekaru biyar da suka gabata.
"Rahotanni sun nuna cewa Azuokeke na son karanta electrical/electronics engineering ne jami'ar Nigeria da ke Nsukka ne (UNN)."
Uba ya bayyana cewa an kafa makarantar ne a ranar 6 ga watan Oktobar 2008 domin samar da gudummuwarta wajen samar da ingantaccen ilimi.
Kamar yadda ya bayyana, makarantar ta fara ne da dalubai 24, amma yanzu tana da dalubai 411.
"Makarantar ta samu nasara kashi 100 a jarabawar "Basic Education Certificate Examination" (BECE) wadda aka kammala ta karshen nan; dalubai uku sun samu A har 11 kowannensu.
"Muna farin ciki da nasarar da muka samu. Sakamakon mu na JAMB abin mamaki ne, sakamakon mu na WASSCE da NECO su ma ba makusa." Kamar yadda ya bayyana.
Post a Comment