Header Ads

Iyalai 1,500 na shirin barin muhallansu sakamakon hare-haren kada da bauna a kasar Mozambik

kada a gabar kogi

Kimanin iyalai 1,500 ne ke shirin barin muhallansu a tsakiyar kasar Mozambik sakamakon hare-haren dabbobin daji, ciki har da kadoji da bauna.

Wani jami'i ya bayyana cewa hukumomi sun tattabar da rasuwar mutane uku sakamakon hare-haren dabbobin daji a cikin watanni uku na shekarar 2023.

Shugaban karamar hukuma a Marromeu da ke yankin Sofala, Henriqueta de Rosario, ya bayyana cewa karamar hukuma za ta canzawa iyalan wadanda hare-haren ke yiwa barazana 1,500 wuri, kamar yadda kafar watsa labaru ta BBC News ta bayyana.

Bauna daga wurin adana dabbobi na Marromeo Special Reserve da ke rafin Zambezi sun kutsa yankin gidajen mutane, inda dole ta sa mutanen suka koma kan tsibiran da ke cikin rafin.

To sai dai bayan sun samu mafaka a kan tsibiran, sai kuma suke fuskantar barazana daga hare-haren kada.

"Fada tsakanin mutum da dabbobin daji na karuwa a zahiri." Kamar yadda Ms Rosario ta bayyana, inda ta kara da cewa mutane da yawa sun fuskanci barazana.

Ta bayyana cewa kusan mutane 400 sun sa hannu su bar wurin domin kashin kan su.

No comments

Powered by Blogger.