Header Ads

Isra'ila ta rusa gine-gine masu yawa a yamma da gabar kogin Jordan wanda aka mamaye da kuma Jerusalem - Rahoton majalisar dinkin duniya

Hukumomin mamaya na Isra'ila sun rusa gine-gine mallakar Falasdinawa 42 a Jerusalem da aka mamaye da kuma yamma da gabar kogin Jordan da aka mamaye , ciki har da gidajen kwana 17, kamar yadda ofishin majalisar dinkin duniya na hadin gwiwa domin ayyukan agaji (OCHA) ya bayyana a cikin sabon rahotonsa. Rushe-rushen na bayan nan an yi su ne a cikin satuka biyu na farko na wannan watan. 

Bayan haka, gine-gine tara a cikinsu masu aikin agaji ne suka bayar da su a wani bangare na aikin agaji, ciki har da makaranta. An rusa su ne kan ikirarin cewa ba su da izinin ginawa da na yin gyara wanda hukumomin mamayar ke bayarwa, kamar yadda rahoton ya nuna. Irin wadannan lasisi na da matukar wahala da tsada ga Falasdinawa su samu, kuma a dukkan yanayi ba a cika samu ba. Yayin da iyalansu ke kara yawa, Falasdinawa da ke yamma da gabar kogin Jordan da aka mamaye da Jerusalem dole ko dai su kara gidan nasu ko kuma su gina wasu sababbi ba tare da lasisi ba.

Mafi yawan rushe-rushen ana harin Area C ne da su, wanda ke karkashin cikakken ikon sojojin Isra'ila. Ciki har da makarantar da masu aikin kawo taimako ke samarwa kudi da ke Bethlehem. Makarantar na da azuzuwa guda biyar da sama da dalubai sittin wadanda ke tsakanin aji daya da aji hudu.

Sauran rushe-rushen kamar yadda rahoton ya nuna, an yi su ne a gabashin Jerusalem da aka mamaye, wanda ya haifar da rasa muhalli ga iyalai bakwai da suka kunshi mutane 39, ciki da yara 22.

Isra'ila ta mamaye gabashin Jerusalem ne yayin yakin kwanaki shida da aka yi a shekarar 1967. Ta mamaye gabadaya birnin a shekarar 1980 a wani yanayi wanda kasashen duniya ba su amince da shi ba.

Bayan rushe-rushen, rahoton ya bayyana cewa daga farkon shekarar nan zuwa 15 ga watan Mayu, sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 108 a yamma da kogin Jordan da aka mamaye, ciki har da gabashin Jerusalem. Wannan ya fi lunki sau biyu na mutanen da suka rasu 51 a daidai wannan lokacin a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ma yi kira kan Isra'ila sakamakon matakan da ta ke dauka wadanda horonsu ke da tsauri kan iyalan wadanda ake zargi da aikata laifuffuka. "Mataki mai tsauri na horon rushe-rushe horo ne babba kuma ba kan ka'ida ya ke ba a kan dokokin kasa-da-kasa, domin ana yin su ne kan iyalan wadanda suka kai hare-haren ko kuma wadanda ake ikirarin sun kai hare-haren." Kamar yadda OCHA ta bayyana.

A karkashin dokar kasa-da-kasa, yamma da gabar kogin Jordan da kuma gabashin Jerusalem yankuna ne da aka mamaye. Saboda haka duk wasu gine-gine domin zaman yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ba kan ka'ida ya ke ba.

No comments

Powered by Blogger.