Header Ads

Isra'ila ta kashe kwamandan Islamic Jihad na biyar

Ahmad Abu Daqqa

Sojojin Isra'ila sun kashe wani babban kwamandan kungiyar fafutikar Falasdiwa ta Islamic Jihar, Ahmed Abu Daqqa, a yayin wasu hare-haren jiragen sama da suka kai a wurare da dama da ke Gaza, awowi bayan kungiyar ta bayyana rasuwar wani babban shugaban mayakansu sakamakon wani hari da kasar ta kai da safe kafin gari ya waye.

Wajen daukar fansa, wani makamin roka da aka harba daga zirin Gaza ya kashe mutum daya tare da raunata akalla mutane biyu a birnin Rehovot da ke tsakiyar Isra'ila, kamar yadda 'yan sandan Isra'ila suka bayyana.

Kamar yadda Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta bayyana, Ahmed Abu Daqqa, wanda shine babban kwamandan bangaren kungiyar da ke rike makamai ta al-Quds Brigades, ya rasu ne sakamakon harin da aka kai a Khan Younis a ranar Alhamis. Mutane hudu ma sun jikkata sakamakon harin.

Shine kwamandan kungiyar Islamic Jihad na biyar da Isra'ila ta kashe tun bayan fara kai hare-haren ta a Gaza da safe kafin gari ya waye a ranar Talata.

Sojojin Isra'ila sun bayyana cewa sun kai hare-hare wurare 158 a Gaza a yayin da akalla makaman roka 523 aka harba daga yankin na Gaza zuwa yankunan da aka mamaye a wannan satin.

Ministocin kasashen waje na Misra, Jordan, Faransa da Jamus duk sun yi kira da a kawo karshen fadan tsakanin Isra'ila da mayakan na Gaza, wadanda ke musayar wuta tsawon kwanaki uku.

Akalla Falasdinawa 123 kawo yanzu sojojin Isra'ila suka kashe a wannan shekarar kamar yadda kididdigar Falasdinawa ta nuna.

No comments

Powered by Blogger.