Header Ads

Iran ta kama wani jirgin ruwa mai dauke da mai wanda ya bugi jirgin ruwan Iran a tekun Oman

Jirgin ruwan da Iran ta kama

Sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kama wani jirgin ruwa mai dauke da mai wanda ke dauke da tutar Marshal Islands a tekun Oman tare da juyo akalarsa zuwa kasar bayan jirgin ya bugi jirgin ruwan Iran tare da kokarin gudu bayan hakan, wanda wannan keta dokokin teku ne.

Kamar yadda sashen hulda da jama'a na bangaren sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana, jirgin ruwan ya bugi jirgin ruwan kamun kifi ne mallakin Iran da yammacin ranar Laraba.

Mutane da dama da ke cikin jirgin ruwan na Iran sun samu raunuka sakamakon al'amarin a yayin da kuma mutane biyu har yanzu ba a gan su ba.

Jirgin ruwan mai dauke da tutar Marshal Islands, bayan faruwar lamarin, sai ya yi yunkuri guduwa daga wurin da al'amarin ya faru, hakan kuma babban keta dokokin kasa-da-kasa ne, domin dokokin sun tanaji samar da kulawa ta magani da samar da magunguna isassu ga wadanda suke cikin jirgin ruwa a yayin da aka samu rashin lafiya ko rauni.

Bayan dai farfadowarsu ne daga rudanin da suka shiga shine masu kamun kifin suka yi kira da a kawo masu taimako.

Jiragen ruwa da ke yin rakiya mallakin kasar Iran, Bayandor, mallakin sojojin ruwa na kasar Iran ne suka kama jirgin bayan samun damar yin hakan daga bangaren hukumar shari'a ta Iran.

No comments

Powered by Blogger.