Header Ads

Ingila na shirin hana ɗaliban Nijeriya da saura zuwa da iyalansu ƙasar

Firaministan kasar Ingila, Rishi Sunak

Kasar Ingila na shirin yin wata sanarwa da a dukkan alamu za ta hana daluban Nijeriya da na sauran kasashe da ke karatu a kasar zuwa da iyalansu.

Kamar yadda wani rahoto na The Sun UK ya nuna, hanawar, wadda za ta shafi duka daluban da ke yin karatun digiri na biyu da kuma sauran karatuttukan gaba da digiri, za a bayyana ta ne a cikin wannan satin.

Sai dai hanawar ba za ta shafi daluban da ke yin digiri na uku ba wadanda kwasakwasan da suke karanta ke tsakanin shekaru 3 da 5 kuma suna da kwarewa sosai, kamar yadda kafar watsa labarun ta Ingila ta bayyana.

Wannan na zuwa ne a yayin wani rahoto da ke nuna cewa yawan mutanen da ke shigowa kasar ta Ingila ya karu zuwa miliyan 1 a yayin da mambobin majalisa masu ra'ayin rikau suka nemi Firaministan kasar ta Ingila, Rishi Sunak, "da ya yi wani abu kan kididdigar mutanen da ke hauhawa." 

Domin rage hauhawar, an bayyana cewa ana sa ran ministocin kasar Ingila za su bayyana wannan kuduri kan shigowar jama'ar a ranar Talata ko Laraba.

Kafar watsa labaru ta The Sun ta bayyana cewa, "Ana sa ran Rishi Sunak zai fito domin yaki da shigowar mutanen - inda ya bayyana cewa kididdigar wadda ya gada ce domin kwanan watan ta na yin nuni ne da karshen Disambar shekarar 2022 - wata biyu kafin ya zama Firaminista.

"Akwai hauhawar mutanen da ke shigowa Birtaniya ta hanyar makalewa da bizar dalubi dan uwansu.

"Dalubai sun shigo da iyalai 135,788 cikin Birtaniya a shekarar da ta gabata - wannan ya lunka sau tara kan na shekarar 2019.

"A shekarar da ta gabata, dalubai 'yan Nijeriya 59,053 sun shigo da iyalansu sama da 60,923. Ya kamata mu tsayar da hakan." Kamar yadda wani dan majalisa mai ra'ayin rikau ya shaidawa The Sun a ranar Asabar.

No comments

Powered by Blogger.