Header Ads

INEC ta rantsar da Isah matsayin kwamishina a karo na biyu

Dakta Mahmuda Isa yana musabaha da Shugaban INEC 

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta rantsar da Dakta Mahmuda Isah a matsayin Zaunannen Kwamishinan Zaɓe, wato 'Resident Electoral Commissioner' (REC) a karo na biyu.

A sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na shugaban hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi, ya raba a Abuja, ya ce an rantsar da kwamishinan ne a ranar Talata a hedikwatar hukumar

Oyekanmi ya ce an gudanar da rantsarwar ne a wajen taron mako-mako na hukumar wanda Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da kwamishinonin ƙasa da sakataren hukumar su ka halarta.

Ya ce a taron, Farfesa Yakubu ya shawarci Dakta Isah da ya ci gaba da sadaukarwa ga al'ummar Nijeriya sannan ya tabbatar a ko yaushe ya na bin hukunce-hukuncen da doka ta gindaya.

Shi dai Dakta Isah, an fara naɗa shi kwamishina ne a cikin Janairu 2018 kuma ya yi aiki a jihohin Jigawa da Kaduna kafin a yi masa canji zuwa Gundumar Babban Birnin Tarayya.

No comments

Powered by Blogger.