Header Ads

Hijabi wata iyaka ce wadda Allah Ya sa - babban malamin Musulunci

Hujjat-ul-Islam Hamid Shahriari

Babban sakataren kungiyar kusancin mazhabobin musulunci ta duniya, Hujjat-ul-Islam Hamid Shahriari, ya bayyana hijabi da wata iyaka wadda Allah Ya sa tare da nuna cewa mata wadanda ke neman makoma mai kyau a lahira ya kamata su mutunta wadannan iyakokin. 

Hujjat-ul-Islam Hamid Shahriari ya bayyana haka ne a yayin taro na uku kan hijabi "Fateme Hijab and Chastity" wanda aka yi a tsarkakken birni na Qom kamar yadda kafar watsa labaru ta Taghrib News Agency (TNA) ta ruwaito.

Malamin ya bayyana cewa mutum zai samu takawa ne da samun matsayi sama da na sauran mutane in har ya bi Annabi Muhammad (S) da Ahlul Bayt (AS). 

Ya nuna cewa rayuwar da ba ta jibanci Allah ba daidai ta ke da zaman kurkuku, inda ya yi kira ga musulmai da su kasance masu bin abubuwan da Allah Ya tsara da Ahlul Bayt (AS) domin su cigaba da rayuwarsu tsarkakakkiya ko bayan rasuwar su.

Kamar yadda Hujjat-ul-Islam Hamid Shahriari ya bayyana, rayuwar gaskiya itace ta bayan mutuwa kuma ta kasance abun al'ajabi ga kowa tunda ba wanda ya san lokacin ta, ingancinta da abubuwan da ke biyowa bayan ta. 

Babban malamin ya bayyana hakan ne yayin taron wanda aka yi kan hijabi "Fateme Hijab and Chastity" wadda kungiyar kusancin mazhabobin musulunci ta duniya ta shirya.

No comments

Powered by Blogger.