Header Ads

Hadimin gidan Sheikh Zakzaky, Malam Jamilu Ya'qub, ya rasu sakamakon hadarin mota

Daya daga cikin hadiman Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) mai suna Malam Jamilu Ya'qub ya rasu sakamakon hadarin mota. 

Malam Jamilu ya rasu ne a kan hanyar sa ta dawowa daga Abuja daga Kaduna a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Kamar yadda ofishin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana, za a yi jana'izarsa ne da karfe 2 na rana, 8 ga watan Mayu na shekarar 2023.
Za a yi jana'izar ne a gidan Marafa, Matazu Road, Sabo Gari, Tudun Wada, Kaduna.

A cikin sakon sanarwar, ofishin na Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi addu'ar Allah Ya amshi uzurinsa, Ya yafe masa, Ya saka shi cikin ceton Annabi da iyalan gidansa tsarkaka. Mu kuma Allah Ya tabbatar da mu bisa tafarkin addinin musulunci har karshen rayuwarmu.

No comments

Powered by Blogger.