Header Ads

Gwamnatin Putin ta haramta wa Barack Obama, sanatocin Amurka da wasu Amurkawa 400 shiga Rasha

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin tare da tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama.

Gwamnatin kasar Rasha a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta haramtawa Amurkawa 500 shiga kasarta, ciki kuwa har da tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama.

Wannan na kunshe ne a cikin martanin Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Rasha kan takunkumin da gwamnatin kasar Amurka karkashin jagorancin shugaban ta na yanzu, Joe Biden, suka kakabawa kasar ta Rasha. 

"A matsayin martani sakamakon takunkumi da gwamnatin Biden ke sa wa ga Rasha akai-akai...an rufe shiga Rasha ga Amurkawa 500." Kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen ta bayyana, inda ta kara da cewa Obama na cikin jerin mutanen.

In dai za a iya tunawa, Amurka ta sa daruruwan kungiyoyi da mutane a cikin jerin wadanda ta sa wa takunkumi a ranar Juma'a a yayin da take kara fadada himmarta wajen yanke tattalin arzukin Rasha sakamakon yakin Ukraine.

"Ya kamata Washington ta sani tun lokaci mai tsawo a baya cewa ba wani matakin cutarwa kwara daya ga Rasha wanda za a bari ba a mayar da martaninsa ba." Ma'aikatar Kasashen Wajen ta bayyana.

A cikin dai mutanen da takunkumin na Rasha ya shafa akwai Stephen Colbert, Jimmy Kimmel da Seth Meyers, bayan nan akwai Erin Burnett na CNN, Rachel Maddow da Joe Scarborough na MSNBC.

Kasar ta Rasha ta bayyana cewa ta sa"Sanatoci, mambobin majalisar Congress da wasu daga cikin mambobin da ke samar da shawara da dubara kan kebantattun abubuwan da suka shafi kasa da matsalolin harkokin kasuwanci "wadanda ke yada dabi'un kiyayya da Rasha da karairayi" da kuma shugabannin kamfanoni "da ke samar da makamai ga Ukraine."

A cikin jawabin, kasar Rasha ta hana shiga ofishin Amurka da ke kare muradanta da 'yan kasarta ga dan jaridar Amurka da aka kulle, Evan Gershkovick, wanda aka kama a cikin watan Maci kan zargin leken asiri.

Hanawar na zuwa me sakamakon rashin gaggawar Washington wajen ba 'yan jaridar da ruka rako Ministan Harkokin Kasashen Wajen Rasha, Sergei Lavrov, biza zuwa majalisar dinkin duniya a cikin watan Afirilu.

No comments

Powered by Blogger.