Header Ads

Girgizar Kasa mai karfin 6.3 ta afku a tsakiyar Japan

Wani gini da ya rushe

Girgizar kasa mai karfin 6.3 ta afku a tsakiyar kasar Japan a yankin Ishikawa ranar Juma'a, sai dai ba a yi gargadin faruwar Tsunami ba kamar yadda masu aikin kula da yanayi suka bayyana. 

Girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 2:42 na rana kuma ta na da nisan kilomita 10 (mil 6) kamar yadda Japan Meteorological Agency ta bayyana.

A cewar Japan Railway, jiragen kasa da ke gudu kamar harsashi na Shinkansen a tsakanin Nagano da Kanazawa, wani sanannen wurin shakatawa, an dakatar da su.

Girgizar kasar na da mataki na shida a ma'aunin shindo na kasar Japan da ke da mataki bakwai a Birnin Suzu da ke Ishikawa, hakan kuma na yin nuni ne da cewa za a iya samun wargajewar kasa mai girma.

Kamar yadda "US Geological Survey" da ke kula da cikin kasa suka bayyana, karfin girgizar kasar shine 6.2.

Dama dai ana ganin girgizar kasa akai-akai a kasar Japan, wadda tana a yankin da ake kira Pacific "Ring of Fire" ne, wani yanki da ke fama da girgizar kasa akai-akai da ya kama daga kudu-maso-gabashin nahiyar Asia zuwa yankin Pacific.

No comments

Powered by Blogger.