Header Ads

Fasinjojin wani jirgi na Max Air su 143 sun tsira bayan tayoyin jirgin sun fashe a Abuja

Sashen tayoyinnjirgin da suka fashe

Tayoyin wani jirgin sama na Max Air sun fashe tare da kamawa da wuta yayin da ya sauka a filin jirgin sama na kasa-da-kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Lahadi.

Al'amarin ya haifar da rudani a filin jirgin saman yayin da ya afku.

Wani jawabi daga "Max Air Flight" ya bayyana cewa a ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 2023, jirgin saman Max Air mai dauke da fasinjoji 143 da karamin yaro daya wanda ya taso daga Yola da kusan 14:10 an shirya zai iso Abuja 15:00. 

"To sai dai tayyoyin jirgin biyu sun fashe a yayin da ya sauka a Abuja, jami'an aikin gaggawa nan da nan suka tarbi al'amarin a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Nnamdi Azikiwe.

"Muna farin cikin sanar da cewa duka fasinjojin da ke cikin jirgin da ma'aikatan ba abinda ya same su. Kamfanin jirgin ya dauki dukkan wasu matakai domin tabbatar da cewa fasinjojin suna cikin walwala kuma ana kula da su a wannan lokacin. An kai su wurin da fasinjoji kan je bayan isowarsu da kayan su da abubuwan da suka mallaka." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

Jawabin ma ya kara da cewa an canza tayoyin jirgin kuma za a yi bincike a kan sa kafin a sake shi domin yin amfani da shi a nan gaba.

"Kamfanin Max Air ya dage domin samar da sufurin jiragen sama mai cikakken kariya wanda kuma za a iya dogara da shi ga duka fasinjoji. Muna godiya ga duka fasinjoji bisa hakurinsu da kuma fahimta bisa abinda ya faru. 

"Kamfanin jirgin na so ya mika godiyarsa ga hukumomin filin jirgin saman, ma'aikatan gaggawa da kuma duka hukumomin da suka tarbi al'amarin cikin gaggawa kuma cikin kwarewa domin tabbatar da cewa duka fasinjojin da ke cikin jirgin babu abinda ya same su.

"Max Air zai cigaba da kawo bayanai a kan al'amarin a yayin da aka samu wadansu bayanan. " kamar yadda ya ke a cikin jawabi na Max Air.

No comments

Powered by Blogger.