Header Ads

Farashin abinci ya karu a duniya a karon farko a cikin shekara daya - hukumar FAO

Hatsi a kasuwanni

Hukumar abinci da aikin gona (FAO) wadda hukuma ce ta majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa farashin abinci ya karu a duniya a watan Afirilu a karon farko a cikin shekara.

Sai dai farashin abinci na nan a kashi 19.6 cikin 100 bayan ya tashi sama a cikin watan Macin shekarar 2022.

A cikin rahoton watan da ya gabata na kididdigar farashin abinci na hukumar abinci da aikin gonar (FFPI) wanda aka wallafa a ranar Juma'a, rahoton ya bayyana cewa a cikin watan Afirilu, farashin abinci kamar nama, siga, shinkafa ya karu wanda ya yi daidai da raguwar kididdigar farashin hatsi, madara da abubuwan madara da kuma mai.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, akwai karuwar kididdigar farashin siga saboda yanayi mara kyau da ya shafi manyan kasashen Asia da ke samar da siga.

"Kididdigar farashin siga ya karu da kashi 17.6 cikin 100 a watan Maci inda ya kai kololuwarsa a watan Oktobar shekarar 2011 sakamakon karancin samar da ita ba kamar yadda aka yi hasashe ba a kasashen Indiya, Sin, Thailand da kuma Tarayyar Turai sakamakon bushewar yanayi da kuma rashin fara girbe rake da wuri a karsar Brazil hade da hauhawar farashin danyen man fetur wanda zai iya kara sawa a nemi ethanol wanda ake samu daga rake." Kamar yadda rahoton ya nuna.

Ana hasashen amfani da hatsi na duniya a shekarar 2022/23 zai kai tan miliyan 2,780, hatsin da aka ajiye a duniya kuwa a karshen yanayi daban-daban ya kai tan miliyan 855.

"In an yi la'akari da wannan hasashe, kashin abincin da aka ajiye domin yin amfani da shi ya kai kashi 29.8 cikin 100, inda ya yi kasa da kashi 30.8 a cikin 100 a cikin watanni 12 da suka wuce, amma ana ganin samar da shi a duniya na tafiya cikin kwanciyar hankali." Cewar hukumar ta FAO.

No comments

Powered by Blogger.