Header Ads

Falasdinawa sun yi taron cika shekaru 75 da fuskantar "bala'i" ko Nakba a yankunan da aka mamaye

Dubunnai sun yi zanga-zanga a gabar yamma da aka mamaye, tare da nuna tutocin Falasdinawa domin tunawa da ranar "Nakba" ko "bala'i" da ya danganci kirkiro kasar Isra'ila. Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, sama da Falasdinawa 76,000 ne suka bari ko aka tursasasu barin muhallansu a shekarar 1948.

A Ramalla, inda nan ne cibiyar hukumar Falasdinawa ta ke, masu zanga-zanga sun dakko alluna bakake da aka rubuta "Return (dawowa)" tare da daga hotunan tsofaffin makullai da ke alamta wahalhalun da Falasdinawa suka shiga tare da neman hakkin su na dawowa. Tunawa da Nakba din a wannan karon na zuwa ne a yayin da ake tsaka da zaman dar-dar sakamakon fada a tsakanin Falasdinawan da Isra'ila inda mutane sama da 170 suka rasa rayukansu a bangarorin biyu tun farko wannan shekara. Mutane 35, wadanda kusan duka Falasdinawa ne, suka rasa rayukansu a kwanaki biyar na fara fada a tsakanin Isra'ila da kungiyoyin fafutika da ke zirin gaza a satin da ya gabata.

An dai kirkiri kasar Isra'ila ne a ranar 14 ga watan Mayu na shekarar 1948 bayan kada kuri'a a majalisar dinkin duniya a cikin watan Nuwambar shekarar 1947 wanda ya raba yankin Birtaniya na Falasdinawa zuwa yankin Yahudawa da Larabawa. Kwana daya bayan ayyana kirkirar kasar Isra'ila, kasashen larabawa biyar suka kai hari kasar, inda kasar ta Isra'ila ta yi galaba kan sojojin larabawa.

A yayin yakin, sojojin Yahudawan sun tarwatsa al'ummu sama da 600 ko suka rage yawansu, kamar yadda kungiyar Yahudawa ta Zochrot ta bayyana. Tun lokacin Falasdinawan ke naman 'yancinsu na dawowa wanda kasar ta Isra'ila ta hana, inda ta ke bayyana cewa hakan na nufin mika wuya ne ga yadda tsarin kasar ta Yahudawa ta ke. 

Kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana, a yanzu akwai Falasdinawa miliyan 5.9 'yan gudun hijira da ke zaune a yamma da gabar kogin Jordan, zirin Gaza, Jordan, Lebanon da Syria. Kasar Isra'ila ta yi bikin samun 'yancin ta karo na 75 a ranar 26 ga watan Afirilu, kamar yadda kalandar Yahudawa ta nuna.

No comments

Powered by Blogger.