Header Ads

Falana ya kai karar shugaban hafsan sojoji da wasu kan kisan wani sufeton 'yan sanda

Mista FeminFalana SAN

Lauyan kare hakkokin bil-adama, Femi Falana SAN, ya shigar da karar shugaban hafsan sojoji "kan kisan sufeto Monday Orukpe a yankin Trade Fair da ke babban titin Legas - Badagry a jihar Legas cikin watan Agustar shekarar 2022 a yayin da ya ke gudanar da aikinsa." 

A cikin karar akwai wasu jami'an sojoji 10 wadanda suma ya ke kara.

A cikin karar wadda aka shigar a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, a maimakon Misis Favour Monday domin tattabatar da hakkin mijin ta na bil-adama na ya rayu, mutuncinsa a matsayinsa na mutum, hakkin sirri da rayuwar iyali da nuna cewa shi ba mai laifi ba ne.

A cikin karar, Falana ya bayyana cewa, "A fili ya ke cewa an keta hakkokin marigayin in an yi la'akari da manyan hujjoji da ke cikin rubutun da aka yi wanda ke tare da rantsuwa domin karfafawa, wanda ke kan doka domin tabbatar da ra'ayin da ke cikin karar." 

Kamar yadda Falana ya bayyana, "Mutum ya kamata a kyale shi ya yi yawo a kasar Nijeriya, ya shaki iskar Nijeriya har sai kotu ta samu bai cancanci yin hakan ba. Jami'an wanda ake karar ba su da hakkin hana rayuwar marigayin kamar yadda ya ke a cikin wannan shari'ar." 

"Muna fatar alkali zai warware matsalolin da suke cikin jawabin da muka hada tare da karar nan. Baki daya dai, muna so alkali ya dubi wannan kara a matsayin wadda ke da madogara kuma bayan ya yi haka ya bayyana tare da bayar da umarnin da ke cikin karar kamar yadda aka nema." Kamar yadda ya ke a cikin wani bangaren karar.

"Wadda ta shigar da karar 'yar Nijeriya ce, mazauniyar Ota da ke jihar Ogun kuma matar Sufeto Monday Orukpe wanda jami'an wanda ake kara na daya suka yiwa mummunan kisa."

"Marigayin, Sufeto Monday Orukpe, Sufeton 'yan sanda ne da ke yankin cibiyar 'yan sanda ta Trade Fair da ke Legas wanda aka kashe a ranar 3 ga watan Agustar 2022, a kan babban titin Legas/Badagry a yayin da ya ke yin aikinsa a matsayinsa na jami'in dan sanda."

"Marigayin na da 'yancin hakkin sa na ya rayu, mutuncinsa a matsayinsa na mutum, a saurari shi ba tare da nuna bangaranci ba da kuma nunu cewa ba shi da laifi wanda sashe na 33, 34, da 36 (1) da (5) na Nijeriya (kamar yadda aka gyara) da Mukala ta 4, 5 da 7 na the African Charter on Human and People's Right (CAP A10) LFN 2004 suka tabbatar masa."

"Kisa ba kan ka'ida ba na mijin wadda ta shigar da kara; Sufeto Monday Orukpe wanda jami'an wanda ake kara na daya suka yi a babban titin Legas/Badagry a ranar Laraba, 3 ga watan Agustar 2022, ya keta hakkin marigayin na ya rayu wanda sashen 33 (1) da tsarin mulkin tarayyar Nijeriya (FRN) 1999 (kamar yadda aka gyara) da Mukala ta 4 na the African Charter on Human and People's Right suka tabbatar masa." 

A cikin karar an dai nemi alkalin kotun da ya bayar da umarni ga wadanda ake karar da su samar da kudi naira miliyan 100 domin ilimantar da yaran sufeton daga matakin firamare har jami'a a duk inda suke so.

Hakazalika, tare da kuma samar da kudi naira miliyan 200 ga wadda ta shigar da karar domin keta hakkoki da dama da aka lissafo a cikin karar na marigayin a matsayinsa na mai kula da iyalinsa tare kuma da sauran abubuwa da dama da ake nema alkalin ya tabbatar da su a cikin karar.

No comments

Powered by Blogger.