Header Ads

Buhari zai kara sati daya a Landan saboda ganin likitan haƙora

Shugaban kasa mai barin gado, Buhari
Shugban kasa Muhammadu Buhari zai cigaba da kasancewa a Landan da ke kasar Ingila har na tsawon sati daya sakamakon bukatar hakan da wani likitan sa na hakori ya yi wanda ya fara duba shugaban kasar.

Wannan na cikin wani jawabi ne wanda mai baiwa shugaban kasar shawara na musamman a bangaren watsa labaru, Femi Adesina, ya yi.

Kamar yadda Adesina ya bayyana, likitan ya bukaci ya duba shugaban kasar na wasu kwanaki biyar ne sakamakon wani aiki da ya riga ya fara yi.

Shugaba Buhari dai ya hadu da sauran shugabannin kasashen duniya ne wajen bikin nadin sarautar Sarki Charles III a ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2023.

A yayin da ya ke Landan, shugaban kasar ya bayyana damakaradiyyar Nijeriya a matsayin wadda ta ke kara girma, inda ya nuna gamsuwa da babban zaben da aka gudanar na shekarar 2023, wanda ya bayyana cewa ya bar darussa da za a koya domin gudanar da zabukan da kyau da ke tafe nan gaba.

A yayin da ya ke jawabi ga takwarorinsa shugabannin kasashe da ke cikin kungiyar kasashe rainon Ingila a matsayin wani bangare na bikin nadin sarautar sarkin na Ingila kuma a matsayin sarkin na shugaban kungiyar, shugaba Buhari ya bayyanawa kungiyar cewa mutane da yawa sun fito yayin zaben, duk da cewa an samu 'yan rigingimu, mutane sun nuna cewa za a iya zaben gwamnati cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da nuna san kai ba.

Shugaban ya kara da nuna rawar da matasa suka taka yayin zaben da kuma taimakon su ga cigaban kasa.

Ya bayyana shigar da matasa da yawa suka yi cikin siyasa da sakamakon kudurin "Not Too Young To Run" ne wanda mulkin sa ya sawa hannu ne ya zama doka.

No comments

Powered by Blogger.