Header Ads

Buhari ya amince da a dage lokacin gudanar da aikin kidaya da za a yi a shekarar 2023

Shugaban Nijeriya Buhari

Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da a dage gudanar da kidayar yawan mutane da ta gidaje ta shekarar 2023 wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin ranakun 3 zuwa 7 na watan Mayun wannan shekarar zuwa wani kwanan watan wanda gwamnati mai zuwa za ta zaba.

An dauki wannan matakin ne a ranar Juma'a biyo bayan tattaunawa a tsakanin shugaban kasar da kuma shugaban hukumar kidaya ta kasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, a fadar shugaban kasa.

In dai za a iya tunawa, an sa cewa za a gudanar da kidayar ne a ranar 27 ga watan Maci, sai aka daga saboda zaben gwamnoni zuwa 3 ga watan Mayu.

A ranar Alhamis, a yayin wata tattaunawa da Jami'an diflomasiyya a Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje a Abuja, shugaban hukumar ya bayyana cewa hukumar har yanzu ba ta gama samun kayan aikin da ta ke bukata domin yin kidayar ba, inda ya bayyana cewa za a kawo wasu daga cikin kayan nan da 'yan kwanaki.

"A kasa baki daya, muna bukatar PAD 800,000, a yanzu mun iya samun 500,000. Sauran za su zo a cikin 'yan kwanaki masu zuwa." Kamar yadda ya bayyana.

A bangaren taimako daga bangaren masu zaman kansu da sauran masu ruwa-da-tsaki a cikin al'amarin, ya bayyana cewa, "Amma ka san yadda suke aiki; ba wai kudi zai zo bane kawai ko yaya. Sai sun yi magana da gwamnatinsu sun kuma yi duba ga kasafin kudin su. Kuma hakan na faruwa a yanzu haka. Amma ba za mu iya cewa wasu kudi sun shigo ba. Mataki-mataki ne, kuma matakin na faruwa a yanzu haka."

No comments

Powered by Blogger.