Header Ads

Buhari ya ƙaddamar da kurkuku ta zamani wadda za ta ɗauki mutane 3,000 a jihar Kano

Wani bangare na kurkukun zamani da aka kaddamar a Kano.

Shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da wata kurkuku ta zamani wadda za ta dauki mutane 3,000 a Janguza da ke jihar Kano.

A cikin jawabin da ya yi ta na'ura mai kwakwalwa, shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gina kurkukun zamanin mai daukar mutane 3000 ne a yankuna shida na kasar nan domin rage cinkoson fursunoni a wasu wuraren kurkukun da kuma kula da su kamar yadda ya kamata bil-adama a kula da shi.

Shugaban kasar ya kara da cewa sabon ginin zai rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen safarar wadanda ke kurkukun wajen zuwa da dawowa kotu, domin sabon ginin na da dakunan kotu biyar domin yin shari'a nan-da-nan.

A cikin jawabinsa, ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbeshola, ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su dauki nauyin ciyar da fursunoni da ke cikin kurkuku mallakin gwamnatin tarayya, domin laifuffukan da aka aikata a jiha. Hakan, kamar yadda ya bayyana, yana kan layin yadda tsarin mulkin tarayya wanda aka gyara ya tanada.

A yayin da ya ke jawabi a maimakon gwamnan jihar Kano, Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alh. Usman Alhaji, ya yi godiya ga shugaban kasar saboda kaunarsa da ayyukansa ga jihar. Ya bayyana fatar sa na cewa sabon gidan kurkukun zai taimaka wajen aikace-aikacen masu gyaran hali. A cikin jawabin sa na godiya, shugaban gyaran hali, Halliru Nababa, ya yi godiya ga gwamnatin tarayya, gwamnati da jama'ar Kano domin goyon bayan su ga aikin tare da kira ga mutanen kasa da su karbi fursunoni da suka dawo cikin jama'a a matsayin mutanen da suka canza, inda ya bayyana cewa idan aka gujesu za su kara fadawa cikin laifuffukan.

No comments

Powered by Blogger.