Header Ads

Biden ba zai nemi gafara kan kisan kiyashin da Amurka ta yi a Hiroshima da Nagasaki ba a yayin ziyararsa Japan

Bam din nukiliya na farko da aka jefa a Hiroshima ya kashe mutane 140,000, a hari na biyu kuma a Nagasaki ya kashe wasu 74,000.

 Biden bai yi niyyar neman gafara ba a yayin ziyara da zai kai kasar Japan nan gaba sakamakon harin bam din nukiliya a biranen Japan na Hiroshima da Nagasaki a shekarar 1945 wanda kisan kiyashi ne da ya kashe mutane sama da 200,000, a cewar mai bashi shawara a fannin tsaro.

A yayin da aka tambaye shi a ranar Laraba ko Biden na da wani shiri na neman gafara sakamakon bama-bamai da Amurka ta jefa a biranen Japan biyu, mai bayar da shawara a kan tsaron kasa a White House, Jake Sullivan, ya amsa a bayyana da "A'a!."

"Shugaban kasar ba zai yi wata magana a Peace Memorial Park ba. Shugaban kasar zai je ne ya hadu da sauran shugabannin kasashen G7 domin sa fulawar girmamawa da kuma sauran wasu al'amurran. Amma wannan, a mahangar sa, ba lokacin wani abu da ya shafi kasashen biyu ba ne. Zai kasance kamar haka ne, daya daga cikin shugabannin G7 ya zo domin nuna girmamawarsa." Kamar yadda Sullivan ya shaidawa manema labaru da ke cikin jirgin Air Force One domin zuwa taron.

A bangare daban kuma a yayin taron manema labaru a fadar White House, wani dan jarida ya tambayi kakakin majalisar tsaron kasa John Kirby ko Biden na da niyyar neman gafara sakamakon harin na nukiliya ko kuma ya yi magana a kan abinda ya faru. Amsar da Kirby ya bayar ta yi kama da wadda Sullivan ya bayar, inda ya amsa da cewa tafiyar Biden ba kan abinda ya faru a baya ba ne amma "a kan abinda zai zo nan gaba ne."

"Shugaban kasar ya shirya kai ziyara wurin tunawa da mutane marasa laifi da suka rasa rayukansu a bam din na nukiliya da aka jefa a Hiroshima." Kirby ya bayyana.

Hiroshima ta yi kaca-kaca sakamakon harin bom din nukiliya irin na Plutonium mai suna Fat Boy a ranar 6 ga watan Agustar shekarar 1945 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 140,000. Kwana uku bayan nan kuma, fashewar bam da ke dauke da sinadarin Uranium mai suna "Fat Man" ya kashe wasu mutanen 74,000 a Nagasaki a cikin kwanakin karshe na yakin duniya na biyu.

Ba a taba samun neman gafara daga Washington a hukumance ba sakamakon jefa bama-baman a biranen na Japan guda biyu ba. Amurka na bi a hankali domin kada ta nemi gafara sai dai ta nuna kaduwa sakamakon yawan asarar da bama-baman suka haifar.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama ne shugaban kasar Amurka na farko da ya fara kai ziyara wurin tunawa da al'amarin a Peace Memorial da ke Hiroshima. Bai nemi gafara ba sakamakon amfani da makamin nukiliyar na farko a tarihi kuma bai nuna rashin karfin matakin da tsohon shugaban kasar Amurka, Harry Truman, ya dauka na haifar da mummunan kisan kiyashin ba.

Amurka a cikin nuna isa na cigaba da nuna dacewar jefa bama-baman da abinda ya biyo baya, inda ta ke nuna cewa sun zama dole domin a kawo karshen yakin tare da "ceton rayuka," duk da cewa masana tarihi da dama na sa alamar tambaya a kan wannan mahangar tare da cigaba da ikirarin cewa ba dalili ba ne.

No comments

Powered by Blogger.