Header Ads

Babban shugaba a Islamic Jihad Khader Adnan ya rasu a kurkukun Isra'ila bayan kwashe kwanaki 87 yana yajin cin abinci

Khader Adnan na Islamic Jihad 

Hukumomin kurkukun Isra'ila sun bayyana cewa wani babban shugaban kungiyar fafutika ta Islamic Jihad, Khader Adnan, ya rasu a cikin kurkukun Isra'ila bayan kashe kwananki 87 yana yajin cin abinci.

Hukumomar gidan kurkukun Isra'ila (IPS) ta bayyana cewa an samu Adnan ba tare da yana iya yin motsi ba a cikin dakin kurkukun sa da ke Nitzan a birnin Ramle da safiyar ranar Talata. 

An kawo shi cibiyar kula da lafiya ta Shamir da ke wajen Tel Aviv, a asibitin ne aka bayyana cewa ya rasu kamar yadda IPS din ta bayyana.

Da sanyin safiyar ranar Lahadi, wata kotu a Isra'ila ta hana sakin Bafalasdinen da ke yin yajin cin abinci duk da cewa yanayin lafiyarsa na kara ta'azzara.

A yayin da take tattaunawa da cibiyar bayanai ta Falasdinawa (PIC) matar Adnan, Randa Mousa, ta tabbatar da cewa kotun Isra'ilan ta ki amincewa da bukatar yin belin mijin nata, inda ta bayyana cewa kotun ta sa wani kwanan watan na ranar 10 ga watan Mayu domin gudanar da zaman shari'a.

Ta yi gargadin cewa halin da mijin ta ke ciki ya ta'azzara sakamakon yajin cin abinci da ya ke yi wanda ya fara a farkon wannan shekarar.

An dai kama Adnan ne a ranar 5 ga watan Fabrairu, kuma nan-da-nan ya shiga yajin cin abinci domin nuna adawa da kamun da aka yi masa.

Ya kasance yana fama da rashin lafiya mai tsanani sakamakon yajin cin abincin wanda ya hada da aman jini, rashin karfi a jiki, rashin sanin halin da ya ke ciki akai-akai, shan wahala wajen yin magana, tafiya, barci da mayar da hankali, da ciwo a duka jikinsa.

A cikin shekaru 20, sojojin Isra'ila sun kama Adnan kusan sau sha biyu sakamakon al'amurransa na siyasa da rashin goyon bayan mamaya. Ya dai yi shekaru takwas a kurkuku.

Ya yi yajin cin abinci sau hudu a yayin da ya ke a tsare. Wanda ya fi tsawo shine wanda ya yi kwanaki 67 yana yi a shekarar 2012 wanda ya sa aka sako shi hakan kuma ya sa wasu Falasdinawa da ke kurkuku bin sahu. 

A shekarar 2015, ya kara yin yajin cin abinci na kwanaki 56 domin yin adawa da kama shi da aka yi. Ya sake yin haka na kwanaki 58 a shekarar 2018. 

An ma kama Adnan a shekarar 2021 inda kuma ya yi yajin cin abinci na kwanaki 25. 

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun bayyana cewa Isra'ila ta karya duk wasu hakkoki da 'yanci na fursunoni da Fourth Geneva Convention ya ba su. Sun ce tsarewar da Isra'ila ke yi da ake kira "Administrative detention" ta karya hakkinsu na bin ka'idoji tunda ba a bayar da dalili ga 'yan kurkukun kuma ana tsare su na tsawon lokaci ba tare da bayyana laifinsu, kai su kotu ko kuma tabbatar da laifinsu ba.

No comments

Powered by Blogger.