Header Ads

Ba ma shirin janye sabbin kudi - Babban bankin Nijeriya

Gwamnan babban bankin Nijeriya

Babban bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa ba ya shirin janye sabbin takardun kudi da suke yawo cikin kasa a yanzu haka.

Daraktan babban bankin na rikon kwarya a sashen sadarwa, Isa AbdulMumin, ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi a ranar Lahadi a Abuja.

Jawabin martani ne ga labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa babban bankin na tunanin janye sabbin takardun kudi na N1000, N500 da N200 da ke cikin kasa a yanzu haka.

"Muna so mu bayyana cewa wannan shaci-fadin ba ya da tushe kuma shiri ne na wasu domin tada hankalin 'yan kasa.

"Tsoffin kudaden da kuma sabbin ana amfani da su a tare.

"CBN na rarraba sabbin kudin masu yawa daga " Nigeria Security Printing and Minting Company Limited." Kamar yadda ya bayyana.

AbdulMumin ya bayyana cewa babban bankin na iyakar kokarinsa wajen ganin ya samar da isassun kudi domin gudanar da tattalin arzuki da kyau.

"Saboda haka muna kira ga jama'ar kasa da su yi watsi da duk wani ikirari na cewa za a janye sabbin takardun kudaden.

"Domin cire kokwanto, sabbin kudin da kuma tsoffin kudin za su cigaba da kasancewa a matsayinsu a tare.

"Za su cigaba da yawo a tare domin kasuwanci kafin wa'adin 31 ga watan Disamba, inda za a janye tsoffin takardun kudin na N1000, N500 da N200." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.