Header Ads

An yi nadin sabon Sarkin Ingila duk da zanga-zangar da aka yi dangane da gidan sarautar

Sarki Charles III a gun bikin nadin sa

Nadin Sarki Charles III a gini mai dadadden tarihi na Westminster Abbey da ke Landan, wanda hakan shine irinsa na farko cikin shekaru masu yawa, ya jawo mutane fitowa zanga-zanga kan tsarin sarautar wadda suke kallo a matsayin wani abu na zamanin da. 

Sarki da kuma sarauniya Camilla an nada su ne a ranar Asabar a wani biki da aka yi wanda baki sama da 2,000 suka halarta, ciki harda shugabannin kasashe, masu sarauta da kuma sanannun mutane.

An ji karar busa kaho (Trumpet) a cikin ginin mai dadadden tarihi a yayin da mutanen da ke nan ke fadin "God save the King!"

Daga wajen ginin kuma dubunnan jami'an tsaro ne, dubunnan daruruwan 'yan kallo da kuma masu zanga-zanga ne suka taru.

'Yan sandan yankin sun kawo jami'ansu mutum 11,500 domin babban aikin tsaro da za su yi a ranar nadin sarautar. An dai ta yin Allah wadai bayan kama mambobin wata kungiya da ba ta kaunar tsarin sarautar, kungiyar na bukatar shugaban kasa ne wanda zabar sa aka yi, kamar yadda mambobin ta shida suka bayyana.

"Ba za mu lamunci kawo tsaiko ba, ko ta hanyar zanga-zanga ko kuma ta wata fuskar." Jami'an 'yan sanda suka rubuta a shafin Twitter a wannan satin. "Za mu hukunta duk wanda ke da niyyar kawo tsaiko ga wannan biki."

Sai dai ko kafin sarkin da sarauniyar su bar fadar Buckingham domin tafiya wajen nadin sarautar a Westminster Abbey, dubunnan masu fafutika da kuma masu zanga-zanga sun taru, inda suka daga alluna da aka rubuta "Not My King" Wato "Ba sarki na bane" a yaren Hausa.

No comments

Powered by Blogger.