An mayar da Siriya cikin majalisar ƙasashen Larabawa - Rahoto
Majalisar kasashen larabawa (Arab League) ta amince da sake mayar da Siriya cikin majalisar mai mambobin kasashe 22 bisa sharadi nan take .
Ministocin Harkokin Kasashen Wajen kasashen larabawan ne suka dauki matakin hakan a yayin wata tattaunawar sirri da suka yi a babban birnij kasar Misra, Cairo, a ranar Lahadi, kamar yadda kafofin watsa labaru suka ruwaito.
Wani dan diflomasiyya na kasar Misra ya shaidawa wata jarida da ke Abu Dhabi the National newspaper cewa dawowar ta kasar Siriya "bisa sharadi ne" inda ya kara da cewa kasancewar ta cikakkiyar mamba a majalisar ya dangantaka ne da dawowar 'yan gudun hijirar kasar Siriya ba tare da samun wata matsala ba da kuma ayyukan siyasa ingantattu a kasar.
Tun a farko, Ministan Harkokin Kasashen Wajen kasar Lebanon ya ba al'amarin dawowar kasar ta Siriya cikin majalisar Kasashen muhimmanci sosai, inda ya bayyana cewa kasarsa na goyon bayan al'amarin.
Abdullah Bou Habib ya bayyana haka ne kafin ya bar Beirut domin zuwa Cairo saboda halartar tattaunawar ta manyan masu diflomasiyyar kasashen larabawa, kamar yadda jaridar yanar gizo ta kasar Lebanon, el-Nashra, ta ruwaito a ranar Lahadi.
Bou Habib ya ma bayyana cewa kasar Lebanon ta mika neman a dawo da kasar ta Siriya cikin majalisar ta larabawa.
Kafofin watsa labarun kasar Saudiyya sun ruwaito cewa wakilan din-din-din na kasashen larabawa a majalisar sun amince da dawowar kasar ta Siriya cikin majalisar ta larabawa a yayin tattaunawar su a ranar Asabar.
A yayin da ta ruwaito wani jawabi daga wata majiyar da ba ta fada sunanta ba, jaridar kasar Saudiyya da ke fitowa kullum ta Okaz ta bayyana cewa tattaunawar ta ranar Asabar ta hadu da nuna goyon baya mai girman gaske na ganin kasancewar kasar Siriya cikin tattaunawa da ake yi a majalisar.
Tun dai cikin watan Macin shekarar 2011 Siriya ta fada cikin yake-yaken 'yan bindiga da asarar dukiyoyi wanda Amurka da kawayenta suka dauki nauyi.
Sai dai a cikin shekarun baya-bayan nan, gwamnatin kasar ta Siriya wadda ke samun goyon bayan kasashen Iran da Rasha, sun samu sun yi nasarar samun iko a kan kusan kowanne yanki daga hannun 'yan ta'addan.
Majalisar kasashen larabawa ta cire Siriya daga cikin ta - wadda Siriya din na cikin wadanda suka kirkiro majalisar - ne a cikin watan Nuwambar shekarar 2011, inda suka bayyana cewa Damascus na tursasawa 'yan adawa masu zanga-zanga. Siriya ta yi watsi da cireta daga majalisar da aka yi inda ta bayyana hakan da "ba kan ka'ida ya ke ba kuma ya karya dokokin majalisar."
A cikin 'yan watannin bayan nan, kasashe da dama da jam'iyyun siyasu sun yi ta kira da a mayar da Siriya din cikin majalisar.
Post a Comment